Messi da Ronaldo da Suarez da Lewandowski: Da tsohuwar zuma ake magani

Manyan 'yan wasan da ke da shekara sama da 30 ne ke zura kwallaye a raga a wasu gasar kasashen Turai da ke nuna cewar har yanzu ruwa na maganin dauda.

Robert Lewandowski ne kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga mai 23 a raga, shi kuwa Luis Suarez da Lionel Messi suna da sha bibiyu a La Liga da Cristaiano Ronaldo mai 15 a Seriae A.

Dukkan 'yan wasan sun haura shekara 30 da haihuwa, amma hakan bai hana su cin kwallaye ba a gasar da suke buga wa a bana ba.

Lashe takalmin zinari

Lewandowski, mai shekara 32, shi ne kan gaba a cin kwallaye a Turai da ake sa ran zai iya lashe takalmin zinare, kuma yana kokari a Bayern Munich.

Suarez, mai shekara 34, yana bayar da gudunmuwa a Atletico Madrid, kuma kwazon da yake yi har wasu na hangen zai iya lashe Pichichi a Spaniya duk da Lionel Messi mai shekara 33 na sa kwazo shi ma.

Cristiano, mai shekara 35, na kara fito da kansa a shirin lashe kyautar takalmin zinare a gasar Serie A da bai taba yi ba tun bayan da ya koma Italiya da taka leda daga Real Madrid.

Wani abun da 'yan kwallon uku suke yi shi ne suna zura kwallo a raga ne a cikin da'irar abokiyar karawa.

Su ukun cin ci kwallo 50 a tsakaninsu, guda biyu daga ciki da Lewandowski ya zura a raga daga wajen da'ira ta 18 ya ci.

Lewandowski ne kan gaba a cin kwallaye da kai wanda keda hudu a raga a bana da kuma cin fenariti biyar.

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo hudu a bugun fenariti, shi kuwa Suarez daya ya ci a bugun daga kai sai mai tsaron raga ya barar da daya a karawa da Eibar.

Sauran gasar kasashen Turai kuwa matasan ne ke kan gaba a cin kwallaye a raga, inda Mohamed Salah mai shekara 28 ya ci kwallo 13 a gasar Premier League a bana.

A gasar Faransa ta Ligue 1 kuwa Kylian Mbappe mai shekara 22 shi ne kan gaba da kwallo 14.

Dan wasa Pedro Goncalves mai shekara 22 shi ne kan gaba a zura kwallaye a raga a gasar Portugal mai 12 kawo yanzu.