Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Anya Lampard zai iya sake samun babbar kungiyar da zai horar?
Yadda Lampard ya kasa nuna bajinta a Chelsea, kungiyar da ya shafe kuriciyarsa, wasu na ganin da wuya ya iya samu wata babbar kungiyar da zai horar.
Frank Lampard ya koma Stamford Bridge a shekarar 2019 ne a matakin kocin Chelsea kan yarjejeniyar wata 18.
Ranar Litinin Chelsea ta bayar da sanarwar sallamar Lampard, bayan da kungiyar ke mataki na tara a teburin Premier League.
Lampard ya taka leda a Stamford Bridge daga 2001 zuwa2014, inda ya buga wasa sama da 420 ya kuma ci kwallo sama da 140.
Tsohon dan wasan tawagar Ingila da ya buga wa Chelsea tamaula sama da 100 ya fara aikin horar da kwallon kafa a Derby County mai buga Championship a 2018 zuwa 2019.
Lampard ya fara aikin jan ragamar Chelsea daga 4 ga watanYulin 2019, wanda ya yi wasa 84 ya ci karawa 44 da canjaras17 aka dok shi fafatawa 23.
Shin ta ƙare wa Lampard ?
Mamba a kungiyar magoya bayan Chelsea, Bashir Hayatu Gentile ya ce Lampard zai iya samu aikin horar wa nan ba da dadewa ba.
''Lampard matashi ne kuma kociyoyin tawagar kwallon kafata Ingila sun tsufa, kuma rawar da ya taka a Ingila da da aikin da ya yi a Chelsea zai sa a bashi aikin horar da tamaula.''
''Kamar yadda ya taka rawar gani a Chelsea a lokacin da kungiyar ke fuskantar kalubale na kashe kudi da kin daukar 'yan wasa da kuma koci, Lamapard ya kai kungiyar Champions League da wasan karshe a FA Cup.
Bashir Gentile ya kara da cewar yanzu lokaci ne na matasan masu horar wa kamar Ole Gunnar Solkskjaer tsohon dan kwallon Manchester United da Mikel Arteta na Arsenal, ya kamata ace Chelsea ta yi hakuri da Lampard zuwa wani lokacin.
Sai dai kuma ya kara cewar a wannan lokaci na kasuwancin tamauala ''Idan Lampard ya ci gaba da zama koci da halin da kungiyar ke ciki da kyar ne idan za ta zama ta hudun farko a Premier kuma hakan faduwa ne.
''Hakika Lampard zai samu kungiya kwanan nan wadda za ta yi hakuri da shi domin ya buga tamaula ya kuma nuna kansa, zai so kuma ya bi sawun masu horar da kwallon kafa da sukas hahara a duniya.''
Ranar Talata Chelsea ta nada tsohon kocin Paris St Germain, Thomas Tuchel a matakin sabon kocinta.
Tuchel zai fara jan ragamar Chelsea a wasan Premier League da za ta yi da Wolverhampton ranar Laraba.