Frank Lampard na takaicin rashin kokarin Chelsea

Frank Lampard ya ce ya damu da rashin kokarin Chelsea, bayan da ta Leicester City ta doke ta 2-0 a gasar Premier League ranar Talata.

Wannan shi ne karo na biyar da aka ci Chelsea a wasa takwas na baya a Premier League, ta kuma koma ta takwas a teburi, yayin da Leicester ta zama ta daya.

"Na damu matuka. Idan ka kwatanta da kokarin da muke yi a baya da wannan matakin da muke kai, koda muka ci Fulham da wasu wasannin da muka yi nasara ya kamata a ce kazonmu ya haura rashin nasara a wasa biyar daga takwas."

Wasannin baya bayan nan da Chelsea ta buga

12 ga watan DisambaEverton 1-0 Chelsea rashin nasara

15 ga watan Disamba Wolves 2-1 Chelsea rashin nasara

21 ga watan Disamba Chelsea 3-0 West Ham samun nasara

26 ga watan Disamba Arsenal 3-1 Chelsea rashin nasara

28 ga watan DisambaChelsea 1-1 Aston Villa yin canjaras

3 ga watan JanairuChelsea 1-3 Man City rashin nasara

16 ga watan Janairu Fulham 0-1 Chelsea samun nasara

19 ga watan Janairu Leicester 2-0 Chelsea rashin nasara

Tun bayan da Chelsea ta doke Leeds a Disamba, kungiyar ta samu maki bakwai daga 24 da ya kamata ta samu.

Ranar Laraba 27 ga watan Janairu, Chelsea za ta karbi bakuncin Wolverhampton a gasar Premier League.