Attahiru Jega: Abubuwa uku da tsohon shugaban INEC ya lissafa kan sake fasalin Najeriya

Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya ce samun shugaba mai adalci shi ne babban abin da ya kamata 'yan kasar su sanya a gaba maimakon ce-ce-ku-cen da ake yi na sake fasalin kasar.
Farfesa Jega ya bayyana haka ne yayin da al`umomin bangarorin kasar ke neman a sake fasalin mulkin kasar ta hanyar komawa ga tsarin lardi-lardi ko shiyya-shiyya, wasu kuma na ganin cewa kamata ya yi a inganta tsarin da ake kai na jihohi 36 da kuma Abuja babban birnin tarayyar kasar.
Tsohon shugaban INEC kuma masanin siyasa, Farfesa Jega, ya shaida wa BBC Hausa cewa ya kamata a inganta tsarin da ake kai na jihohi 36 da Abuja.
Ga abubuwa uku da Farfesa Jega ya lissafa kan sake fasalin Najeriya:
Tsarin jihohi 36 da Abuja
Masanin kimiyyar siyasar ya ce yana ganin zai fi dacewa a ci gaba da tsarin jihohi 36 6 da kuma Abuja babban birnin tarayyar kasar maimakon komawa ga tsarin lardi-lardi ko shiyya-shiyya da ake da su a shekarun baya.
A cewarsa: "Mafi yawanci abubuwan da suke cewa a yi (na komawa tsarin shiyya-shiyya) zai yi wahala idan ma zai yiwun... zancen wai a koma tsohon tsari bai ma taso ba. Harkar duniya a yau komai ci gaba ake yi, don haka ma dai duba bayan mu ga wanne darasi za mu dauka domin mu gina gaba."
Ya kara da cewa yi wa tsarin jihohi 36 da Abuja kwaskwarima shi ne mafita.
"Mu dauki tsarin jihohi 36 amma a rage yawan aikin gwamnatin tarayya, a rage kudin da ake ba ta saboda ayyukan da take yi a bai wa jihohin nan," in ji shi.
Yadda za a rage tabargazar da gwamnoni suke yi
Farfesa Jega ya ce duk da yake yana da ra'ayin rage ayyukan gwamnatin tarayya domin a bai wa jihohi, akwai kuma bukatar fitar da tsarin da zai sanya ido kan tabargazar da gwamnatotcin jihohin suke yi.
A cewarsa: "Babban kalubale shi ne yadda wasu gwamnonin nan namu suke da irin tabargazarar da muka ga suna yi da kudin al'umma d rashin tunani da son kai da son rai, idan aka ce a karo mus aiki za su iya yin wannan abin kuwa?"
Amma ya ce za a rage irin wannan tabargaza da gwamnoni suke yi idan aka jajirce aka zabi mutane masu mutunci da adalci.
"Mutane suna ganin abin yana da wuya, amma gaskiya idan aka tashi aka jajirce aka yi shiri na gaske, a kowacce jiha ba za a rasa mutanen kirki da za a tsayar ba kuma mutane su tallafa musu ta hanyar zabe, su tabbatar an ba su mulki na jiha yadda za su tafiyar da al'amuran jama'a da sadaukar da kai da tabbatar da adalci, " in ji Farfesa Jega.
Ya kara da cewa kodayake ana zargin wasu mutane suna sayar da 'yancinsu wajen zaben bara-gurbi amma abubuwa suna sauyawa "domin mutane ba dabbobi ba ne."
Raba Najeriya
Tsohon shugaban INEC ya ce masu rajin raba Najeriya ba su san kalubalen da za su fuskanta ba idan an yi hakan shi ya sa suke wannan fafutika yana mai cewa zaman Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa shi ne mafi alheri.
Ya ce: "Ni a ganina zaman Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa yana da amfani kuma shi ne muhimmin abu ga duk dan Najeriya a halin yanzu. Matsalar da za ta biyo bayan raba kasar nan wato tana da yawa. Ta fi alfanun da wasu suke hangen za su samu idan kasar nan ta rabu. Don haka gaskiya dole mu dukufa mu yi 'yan gyare-gyaren da suka kamata...zaman lafiya ake so. Idan aka samu zaman lafiya sai ka ga an samu walwala."











