Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Biden ya gabatar da shirinsa na yi wa dukkan Amurkawa rigakafi
Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden ya gabatarwa Amurkawa shirinsa na tabbatar da cewa dukkansu sun samu rigakafin cutar korona yayin da ake ci gaba da samun sabbin mutanen da ke kamuwa.
Biden wanda ake sa ran rantsarwa ranar Laraba, ya ce abin da zai sanya a gaba da farko shine ganin cewa an yi wa duk wanda ya haura shekara 60 a duniya rigakafin cikin gaggawa.
Sannan ya ce gwamnatinsa, za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatocin jihohi domin buɗe ƙarin cibiyoyin yi wa mutane rigakafi.
Mista Biden ya ce ya yi imanin cewa a shirye Amurkawa suke su bawa gwamnati haɗin kai don yaƙi da annobar.
Ya roƙi dukkanin ƴan ƙasar su ci gaba da sanya takunkumi a kwana 100 na farkon gwamnatinsa.
Amurkawa ce ta fi yawan waɗanda suka kamu da cutar a faɗin duniya, sannan yawan waɗnda cutar ta kashe a ƙsar ya zarce na kowacce ƙsa a duniya.
Ya ce tsarin da gwamnatinsa za ta bijiro da shi shine na ganin cewa dukkanin ƴn ƙasar sun samu rigakafin a kyauta ba tare da biyan ko sisi ba.
Ya kuma soki yadda ake sa mun tafiyar hawainiya a shirin raba rigakafin a duk faɗin ƙasar, ƙarƙashin gwamnatin shugaba mai ci a yanzu, wato Donald Trump.
Yayin jawabin nasa, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya kuma soki wasu ƴn jam'iyyar Republican dangane da al'adar ƙin sanya takunkumi yayin da suke harkokinsu a majalisar wakilai.
''Abin takaici ne mutanen da ya kamata su zama abin koyi ga sauran ƴan ƙasa sun zama sune ake faɗkarwa dangane da muhimmancin takunkumi, ya kamata ku canja hali'' inji Biden.