Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matashin da ƙuncin rashin ƙasa a Kuwait ya sa ya cinna wa kansa wuta
- Marubuci, Daga Sumaya Bakhsh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Monitoring
Lokacin da Hamad mai shekara 27 ya cinna wa kansa wuta a kasar Kuwait a watan Disamba, ya jefa fargaba a fadin kasar.
Ƙaramar ƙasar mai arzikin fetur a yankin Gulf kamar almara ne ga yanayin da har wani zai aiwatar da irin wannan mummunan aiki. Amma Hamad ɗaya daga cikin ƴan Bidoon ne da ba su da ƙasa.
Bidoon kalmar Larabci ce da ke nufin "babu" - ba tare da wata ƙasa ba, wanda ga al'umma ke nufin masu fuskantar rashin samun damar shiga al'umma, ba su da matsayi, ma'ana rashin hanyoyin samun ilimi, kiwon lafiya da kuma ayyukan yi. Kuma ga Hamad da danginsa cikin yanayin ƙunci ba su da wata cikakkiyar fata.
'Komi ya rufe'
Kilomita goma sha bakwai daga wajen birnin Kuwait, Sulaibiya wata duniya ce da ke nesa da manyan kantuna da manyan gine-ginen gilashi masu tsayi a babban birnin ƙasar.
Omar na rayuwa ne da iyayensa, da ƴan uwansa 10 da danginsu, a wani matsakaicin gida mai ɗaki biyar a wani rukunin gidaje na matsugunin mafi yawanci ƴan Bidoon.
Matashin mai shekara 33 ya fi kusanci da ƙaninsa, Hamad.
"Mutum ne mai alheri, yana da wayo, ko da yaushe kuma yana murmushi," in ji Omar.
Amma kimanin shekara ɗaya da ta gabata, matashin ya sauya, ya killace kansa a ɗakinsa kuma ya ƙi amincewa a fitar da shi daga gida.
Omar ya san zafin da yake ji. "Komi ya rufe masa."
Batun ƴan Bidoon a Kuwait ya samo asali ne tun 1961, lokacin da wasu da ke zaune kan iyakokin ƙasar ba su nemi izinin zama ƴan ƙasa ba bayan samun ƴancin ƙasar daga Birtaniya.
Sauran ƙasashen Larabawa kamar Saudiyya da Daular Larabawa su ma suna da irin waɗannan marasa ƙasa, waɗanda galibinsu asalinsu makiyaya ne waɗanda ke zaune amma suka ƙi neman zama ƴan ƙasa lokacin aka kafa ƙasa.
Wani ɓangaren kuma, wasu sun rasa ƙasa ne bayan da gwamnati ta soke masu zama ƴan ƙasa, kamar Bahrain inda wasu da dama aka masu izinin zama ƴan ƙasa.
Batun ya kasance wani lamari mai sarƙaƙiya ga gwamnatin Kuwait, wacce ta ayyana Bidoon a matsayin "mazauna ba bisa ka'ida ba."
Ta ce mutum 34,000 ne kawai daga sama da 100,000 da basu da ƙasa a ƙasar da suka cancanci neman izinin zama yan ƙasa kuma sauran ƙabilu ne na wasu ƙasashe.
Gwagwarmayar yau da kullum
Bayan Hamad ya kammala karatunsa na firamare, ya kasa shiga makaranta ta gaba saboda asalinsa na Bidoon. Iyayensa ba su da ƙarfin ɗaukar nauyin karatunsa.
Yaron ya girma yana kallon mahaifinsa da ƴan uwansa suna samun kuɗin da ba tabbas sun saye da sayar da motoci; za su sayar da mota ɗaya a wata ɗaya kuma su ci gaba da fafutika a wasu watanni huɗu.
Kamar ya fahimci cewa ba irin rayuwar da yake buƙata ba ce. Ɗan uwansa ya ce burinsa shi ne ya shiga aikin soja.
Amma ba shi da wannan damar, Hamad ya yi duk abin da zai iya yi, da farko ya sayar da kankana a kan titi har sai da hukumomi suka kama shi.
Ya kuma yi ƙoƙarin kiwon tantabaru da yake saya kan rabin dinari, amma daga baya ya daina bayan ya gano cewa idan ya je sayarwa yana hasara.
Bayan Hamad ya kammala zaman gidan yari na watanni takwas kan satar tunkiya ya sayar, wani ɗan uwansa Jasem ya yi ƙoƙarin samar masa da takardun tafiya inda ya ɗauke shi zuwa Moroko.
Omar ya ce hutun wata dama ce ga ɗan uwansa na samun wata sabuwar rayuwa.
"Ya ga duniya, ya ga rayuwa, kuma ya samu farin cikin. Ya shafe mako uku a can, amma kamar ya yi shekara uku a can. Ya yi kusan shekara biyar yana ba da labarin tafiyarsa zuwa Moroko.
Kisan kai
A baya-bayan nan, Hamd ya shaida wa mahaifiyarsa cewa yana son ya gina rayuwa, yana son ya yi aure. Amma saboda yanayin da suke ciki na rashi, babu wani tallafi da ta yi masa alƙawali illa ta tunatar da shi cewa "Allah zai bayar."
Omar ya ce ya sha yin magana game da kashe kansa amma ƴan uwansa ba su taba yarda da maganarsa ba ko tsammanin zai aikata haka ba, sai wata rana da safe, a wani yanayi na rashin jin dadi, ya cinna wa kansa wuta.
Saboda abin da ya faru, ɗan majalisa Marzouq al-Khalifah ya yi kira ga gwamnati da kafa kwamiti domin nazari kan abin da ke haddada yawan kisan kai tsakanin yan Bidoon.
"Muna cikin ƙasa mai albarka... amma duk da haka mutane suna kashe kansu saboda mawuyacin halin rayuwa da ƙuntatawa rayuwarsu ta yau da kullum.
Mai rajin kare haƙƙin Bidoon Abdullah al-Rabah ya ce yana son ganin an ba ƴan Bidoon 34,000 ƴancinsu na zama ƴan ƙsa kuma sauran a ba su ƴancinsu, wanda zai ba su damar yin rayuwarsu.
Matashin mai shekara 35 ya kara da cewa shi da wasu irinsa suna nuna biyayya ga ƙasar da aka haife su amma ya fahimci girman takaicin matasa a cikin al'ummarsu.
"Wannan matasan ƙarni na uku ne ba tare da magance matsalar ba, har yaushe za su jira? Tabbas ya shafe su."
Ga Omar, abin da kawai yake buƙata shi ne ya kasance a gefen, dan uwansa
Ya saba yakan fita daga Sulaibiya idan ya samu, don ya manta damuwarsa kuma ya ɗauki lokaci a gaɓar teku shi kadai.
Amma yanzu a ko wace rana, yakan ziyarci asibiti don ya dinga duba Hamad ta tagar dakinsa da yake jinya.
Yana jiran tsammani, tare da fatan likita zai fito da labari mai daɗi
An sauya dukkanin sunaye a wannan rahoton don kare su.