Najeriya: 'Yan sanda sun ce sun kama bindigogi fiye da 3,000 a 2020

..

Asalin hoton, NIGERIA POLICE

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta kama muggan masu laifi da dama da take zargi da kuma bindigogi da albarussai a shekarar 2020 da ta gabata.

Rundunar ta bayyana irin nasarorin da ta samu a shekarar 2020 cikin wata sanarwa da kakakinta Frank Mba ya aikawa BBC ranar Litinin.

Sanarwar ta ce ta kama muggan masu laifi da suka kai 21,296 a shekarar 2020 tare da ƙwato bindiga 3,347 da kuma albarussai 133,497.

Ƴan sandan na Najeriya kuma sun ce sun kama motocin sata 960 tare da kuɓutar da mutum 1,002 da aka yi garkuwa da su.

Sai dai rundunar ƴan sandan ba ta yi cikakke bayani ba game da yadda ta kama makaman da kuma inda ta kama su, ko da yake a cikin sanarwar ta ce ta kama babban jagoran fashi da makami.

Rundunar ta kuma ce a halin yanzu daga cikin alƙawalin da ta ɗauka na ƙara ƙaimin yaƙi da laifuka a Najeriya ta kama wasu da ta ke zargi ƴan fashi da makami da masu satar mutane da shannu guda 18 a yayin da shekarar 2020 ke ƙarewa.

Cikin waɗanda ta kama har da wani shugaban ƴan fashi da makami Abubakar Umaru da ake kira Buba Bargu da take zargi da jagorantar fashi da makami a hanyar Abuja - Kaduna da kuma Abuja - Lokoja

Daga cikin makaman da ta ce ta kama sun ƙunshi bindigogi ƙirar AK47 da albarussan bindigar 236.

A cikin sanarwar babban Sufeton ƴan sandan Najeriya MA Adamu ya tabbatar wa ƴan Najeriya da ingantaccen tsaro a shekarar 2021.

Ya jaddada cewa rundunar ƴan sandan ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen yaƙar dukkanin nau'ukan laifuka musamman satar mutane da fashi da makami da satar shanu da sauran laifuka da suka shafi kutse a intanet a shekarar 2021.

Rundunar ta ce za ta gurfanar da waɗanda ta kama a kotu domin fuskantar shari'a.

Matsalolin tsaro a Najeriya sun fi ƙamari a yankin arewacin ƙasar inda ƴan fashi masu satar mutane suka addabi yankin arewa maso yammaci baya ga Boko Haram da ta shafe shekaru tana kai hare-hare a yankin arewa maso gabashi.