Donald Trump: Abubuwa shida da shugaban Amurka zai rasa idan aka tsige shi daga kan mulki

Asalin hoton, Alamy
Yayin da ake shirin rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden, wani batu da ke ɗaukar hankali yanzu a Amurka shi ne batun tsige shugaba mai barin gado Donald Trump
Ƴan kwanaki ƙalilan ne suka rage wa Trump a kan mulki.
Majalisar wakilan ƙasar ta ba mataimakinsa Mike Pence zaɓin ko dai ya shawarci mai gidansa ya yi murabus ta ruwan sanyi, ko kuma a aiwatar da sashe na 25 na kundin tsarin mulkin ƙasar da ke nufin sauke shugaban ƙasa yayin da aka lura ba shi da cikakkiyar lafiyar ci gaba da jagoranci, ko kuma majalisa ta tsige shi.
Yanzu dai abin da ya bayyana a fili shi ne Mista Pence ba shi da niyyar aiwatar da sashen na 25, sannan Trump ba shi da niyyar sauka daga kan mulki.
Don haka ne majalisar wakilan ƙasar ta fara shirinta na tsige Trump daga kan mulki kamar yadda ta lashi takobin yi.
Majalisar ta gabatar da shirinta a hukumance, wanda shi ne mataki na farko na tsige duk wani shugaban da ludayinsa ke kan dawo.
Idan har haka ta tabbata, shugaba Trump zai kasance mutum na farko a tarihin Amurka da aka taɓa tsigewa har sau biyu.

Me ya sa ake son tsige Trump a yanzu ?
Abin da ya faru a majalisar dokokin Amurka ranar 6 ga watan Janairun 2021, abu ne da tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba.
A wannan rana ne dubban magoya bayan Trump suka kutsa majalisar dokokin ƙasar yayin da ta ke zaman tabbatar da Biden a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, suka fasa ƙofofi fa tagogi da lalata ginin majalisa, tashin hankalin da ya janyo mutuwar aƙalla mutum biyar.
Yayin da jami'an tsaro suka bazama wajen neman mutanen da suka yiwa majalisar kutse, yan jam'iyyar Democrat na ganin cewa bai kamata a ƙyale wanda suke zargin ya angiza su ba, wato Trump.
Tun kafin zuwan ranar ne shugaba Trump ya gayyaci dukkan magoya bayansa su taru a Capito Hill, inda majalisar wakilan ƙasar za ta tabbatar da Biden domin neman ta yi watsi da sakamakon zaɓen da shi da magoya bayansa suke kallo a matsayin ƙwace.
Ƴan jam'iyyar Democrat na ganin cewa babban abin da za su yi su ramawa kura aniyarta shi ne tsige shugaban, ta yadda zai zamo shugaba na farko da aka tsige sau biyu.
Wata riba ta tsige Trump ɗin kuma da suke hangowa ita ce idan har majalisar dattawa na iya amincewa ta hana shi riƙe duk wani muƙami, ko ma sake tsayawa takara a nan gaba.

Shin zai iya yafe wa kansa?
Mutane da dama na ta muhawara dangane da mutanen da Trump ya yafe wa a baya, da kuma waɗanda zai iya yafewa a nan gaba.
Yayin da wasu ke ganin zai iya yafe wa kansa, to ko da zai iya yin hakan, ba dai ya yafe wa kansa don gudun tsigewa ba.
Dalili kuwa shi ne laifin tsige shugaban ƙasa babban laifi ne, sannan ita kanta afuwar da shugaban ke da ikon yi wa wasu ta tsame wannan laifi daga ciki.

Shin zai ci gaba da samun kulawar jami'an tsaro?

Kan wannan ya kamata Trump ya gode wa Obama, tun da shi ne shugaban da ya samar da wata doka da ta bada damar kare duk tsohon shugaban ƙasa har karshen rayuwarsa.
Sannan wannan doka ba ta tsame kowanne tsohon shugaban kasa ba bisa wani dalili ko kowanne sharadi ba, don haka ba laifi bane idan an ce Trump zai ci gaba da samun kulawar jami'an ysaro har ƙarshen rayuwarsa.

Ko zai ci gaba da samun alawus ?
Duk lokacin da shugaba ya bar Ofis yana da damar samun wasu fa'idoji da suka haɗa da fansho da ake tunanin zai kai kimanin Dala dubu dari biyu a shekara, da alawus na tafiye-tafiye da yawansa ya kai Dala miliyan daya da kuma kudin ma'aikatansa.
Sai dai duk shugaban da aka sauke daga kan mulki ba shi da damar samun wadannan faidoji.
Don haka matsawar ba majalisar dattawa ba ce ta amince da sauke Trump daga kan mulki, zai ci gaba da karɓar alawus dinsa ko da kuwa ya sauka.

Za a iya kai shi kotu saboda rikicin Capitol Hill ?
Tun da yake tsigewa ba shari'a ba ce, ana iya gurfanar da Mista Trump kan irin ayyukan da suka sa aka tsige shi.
Kundin tsarin mulki ya ce: "Duk wanda aka tsige, yana kuma iya fuskantar tuhuma a kotu kan laifin da ya sa aka tsige shi bisa doka."
Kamar Trump da ake zargi da ingiza rikicin majalisa, zai iya fuskantar shari'a a kan wannan laifi, har ma ya fuskanci hukunci idan aka same shi da hannu.

Za a iya samun shi da laifi a sauke shi ?
Lissafin majalisar ba zai tabbata ba har sai an kaɗa kuri'a tukuna, amma da alama Mista Trump zai kasance shugaban ƙasa na farko da aka tsige sau biyu.
Ƴan jam'iyyar Democrats sun ci gaba da rike ikon Majalisar Wakilai a watan Nuwamba, kuma wasu ƴan jam'iyyar Republican sun ce suna tunanin ƙarfafa yiwuwar tura batun ga majalisar dattawa.
Majalisar dattijai wani lamari ne daban.
Yayin da Mista Trump ke kan mulki, jam'iyyarsa ta Republican ce ke da rinjaye. Amma da zarar Mr Biden ya hau kujera Majalisar Dattawa za ta mika wuya ga ikon Democrats saboda gagarumar nasarar da ta samu a jihar Georgia.
Tare da buƙatar rinjayen kashi biyu bisa uku, akwai bukatar yan Republican da dama su amince da wannan yunƙuri kafin a sauke shugaban.













