Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan Democrats sun matsa wa Mike Pence lamba ya tsige Trump daga ofis
Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ci gaba da matsa lamba ga mataimakin shugaban ƙasar Mike Pence domin ya tsige Donald Trump daga mulki, game da rawar da ya taka kutsen da magoya bayansa suka yi a ginin Capitol na majalisun ƙasar.
Ana sa ran 'yan majalisar za su samu mafita ta neman Mista Pence ya yi amfani da sashen doka na 25 ya tabbatar da cewa Trump bai dace ya ci gaba da shugabanci ba.
Sai dai da alama Mista Pence bai amince da wannan shawara ba.
Kuma matuƙar ya ƙi yin hakan, jam'iyyar Democrat za ta kaɗa ƙuri'ar cire Trump wanda ya tunzura magoya bayansa su afka ginin Capitol.
Shugaban wanda ɗan jam'iyyar Republican ne na shan suka daga 'yan jam'iyyar Democrat da kuma 'yan jam'iyyarsa kan wannan zanga-zanga, bayan boren da aka yi saboda yawan nanata ƙin amincewa da zaɓen shugaban ƙasar da aka yi da Shugaba Trump ke yi. An kashe mutum biyar yayin harin da aka kai ciki har da wani ɗan sanda da ke aiki a majalisar dokokin.
Trump bai dai yi wani bayani ba ga mutane tun bayan dakatar da shi da aka yi daga amfani da shafukansa na sada zumunta cikin har da Twitter a ranar Juma'a.
An tsara zai bar ofis a ranar 20 Janairun da muke ciki, ranar da za a rantsar da shugaban jam'iyyar Democrat Joe Biden a tsayin sabon shugabar. Mista Trump ya ce ba zai halarci bikin rantsuwar da Joe Biden ba.
Misis Pelosi ta rubuta wa 'yan majalisar dokoki cewa, majalaisar wakilai za ta gabatar da bukatar neman Mista Pence ya yi amfani da sashen dokar na 25 a kundun tsarin mulki domin neman tsige Trump daga muka minsa shi kuma ya zama shugaban rikon kwarya.
Majalisar wakilan na da damar kaɗa kuri'a a ranar Talata. Daga nan kuma sai a bai wa Mista Pence da sauran muƙarrabai kwana guda su yi wani abu kan buƙatar
"Za mu yi komai cikin gaggawa, saboda wannan shugaban na neman zaman wata barazana gare mu baki ɗaya," Kamar yadda Pelosi ta rubuta a wasiƙarta ta ranar Lahadi. "Wannan tashin hankalin da koma bayan da muka gani game da dimokraɗiyyarmu da shugaban nan ya janyo na da mukatar ɗaukar matakin gaggawa".
Duk da cewa Mista Pence ya nuna sun raba gari da Shugaba Trump a ranar Lahadi bayan ya bayyana aniyarsa ta halartar bikin rantsuwar da Trump ya ce ba zai je ba, amma babu wata alama da ke nuna zai iya yarda da a tsige shugaban.
A gefe guda kuma ɗan majalisar na biyu a Republican Pat Toomey na Pennsylvania ya ce "Shugaban ya yi murabus cikin gaggawa", haka Lisa Murkowski ta Alaska ta goyi bayan shi.
Me zai faru idan Pence ya ki yin abin da aka bukata?
'Yan Democrat na majalisar wakilai za su ci gaba da shirin cire shi cikin gaggawa. Cire shi a wannan mataki na nufin a gabatar da tuhuma ga majalisar dattijai, kuma Pelosi ta ce za su gabatar da tuhuma kan Mista Trum na "tunzura magoya bayansa su yi bore".
Wasu manyan jigajigan 'yan majalisar sun ce za a gabatar da ƙuri'ar tsige Trump a tsakiyar wannan makon. Idan hakan ta fara Trump zai zama shugaban Amurka na farko da aka tsige a tarihi har sau biyu.
Sai kuma a gabatarwa majalisar dattijai inda zai gurfana gaban kotu, idan aka samu kashi biyu cikin uku sun amince da a tsige shugaban. Kuma idan aka tabbatar da hakan majalisar dattijai za ta yi kuri'ar haramta masa rike duk wani ofishin gwamnati.
Haka kuma, mai tsawatar majalisar James Clyburn wanda kusa ne a Democrat ya shaida wa CNN cewa, jam'iyyar ba za ta aike wa majalisar dattijai wani bayanin tuhuma ba har sai bayan Joe Biden ya kwashe kwanakinsa 100 na farko a ofis, "domin ba shi damar ƙaddamar da ayyukan da ke gabansa."
Me ake ciki game da binciken da ake kan zanga-zangar?
Yayin da masu bincike ke yunƙurin gabatar da waɗanda aka kama da shiga ginin Capitol, Ita kuma rundunar 'yan sanda ta Virginia da Washington ta dakatar da wasu jami'anta saboda zargin halartar zanga-zangar ranar da ba sa aiki.