Trump ya ce ba zai halarci bikin rantsar da Biden ba

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ba zai halarci bikin rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban kasa ba, a ranar 20 ga watan nan.

"Ga duk masu tambaya, ba zan je bikin rantsuwa ba ranar 20 ga watan Janairu," kamar yadda shugaban ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Mista Trump na fuskantar kiraye-kirayen cire shi daga ofis bayan da mutum biyar suka mutu lokacin da magoya bayansa suna kutsa cikin ginin majalisar dokokin ƙasar.

Mutuwa ta baya-bayan nan sakamakon lamarin ta wani ɗan sanda ne Brian Sicknick, wanda ya ƙarasa bayan kai shi asibiti sakamakon raunukan da ya ji.

Hukumar leƙen asiri ta FBI a Washington ta ce za ta yi aiki da ƴn sanda don binciken dalilin mutuwar tasa, duk da cewa ba su bayyana ko za a ɗauki lamarin mutuwar a batun laifin kisan kai ba.

RIkicin na ranar Laraba ya faru ne sa'oi kaɗan bayan da Mista Trump ya goyi bayan magoya bayansa da su yi fito na fito da sakamakon da majalisa za ta gabatar na tabbatar da nasarar Biden a zaɓen watan Nuwamban 2020.

Bayan da ya sha matsin lamba, daga baya Mista Trump ya saki wata sanarwa da aka naɗi muryarsa a yammacin ranar Alhamis yana Allah-wadai da harin da aka kai Capitol ɗin.

Shin Trump ya yi daidai da ya ce ba zai je rantsuwar ba?

Abin da Trump ya yi wani bambaraƙwai ne da ba a saba gani ba: shugaba na ƙarshe da ya taɓa irin haka shi ne Andrew Johnson, a shekarar 1869.

Mista Trump a yanzu ya amince da shan kayen 3 ga watan Nuwamba kuma ya yi alƙawarin miƙa mulki cikin lumana. Sai dai fa har yanzu bai daina zargin an tafka maguɗi a zaɓen ba.

Manyan ƴan majalisa na jam'iyyar Democrat sun nemi mataimakin shugaban ƙasa Mike Pence da ya fara bin matakan tabbatar da cewa Mista Trump bai cancanta ya ci gaba da zama a kujerarsa ba.

Shugabar Majalisar Wakilai Nancy Pelosi da Shugaban ƴan jam'iyyar Democrat na majalisar dattijai Chuck Schumer sun ce a cire Trump daga kujerarsa don "tunzura mutane da take dokokin rantsuwar shan mulki."

A wata sanarwa ta haɗin gwiwa da suka fitar sun ce: "Halayyar shugaban mai haɗari sun sa lallai ana bukatar cire shi daga mulki."

Sun yi kira da cewa a yi amfani da sashe na 25 na kundin tsarin mulki don cire Trump daga mulki, sashen da ya bai wa mataimakin shugaban ƙsa damar maye gurbin shugaban idan har ya gaza yin ayyukansa yadda ya kamata.

Sai dai babu alamar Mista Pence zai yi hakan.

Idan bai yi ba, Mrs Pelosi da Mr Schumer sun ce za su fara bin matakan tsige shi.

Sai dai babu isasshen lokacin yin hakan, cikin kwana 12 da suka yi wa Trump saura a karagar mulkin.

A ranar Juma'a, Mrs Pelosi ta ce ta yi magan da babban jami'in sojin Amurka, shugaban rundunonin sojin ƙsar, da ya hana Mista Trump makullan nukiliya.

A hannu guda kuma, daya daga cikin ma'aikatan Mts Pelosi ya ce an sace wata komfuta daga ofishinta a lokacin da ɓata garin suka shiga majalisar.

Sharhi

Sanarwar da Trump ya yi cewa ba zai halarci bikin rantsar da Biden ba tare da karya al'adar Amurka bai zo da mamaki ba.

Sai a baya-bayan nan ne cikin rashin karsashi ya yarda da shan kayensa, bayan da ya shafe tsawon lokaci yana zargin cewa an yi masa maguɗi.

Saƙon da ya wallafa a Tuwita ya sha bamban da abin da ya faɗa jiya a Fadar White House cewa komai ya wuce. Hakan na nuna cewa Trump bai karɓi ƙaddararsa da zuciya ɗaya ba.

Sannan ba zai yi wa Biden maraba zuwa Washington ba kamar yadda ya alƙawarta cewa za a miƙa mulki cikin lumana. Ga alama ba ma zai zauna kusa da Washington ba a yayin da Biden zai isa fadar.

A maimakon haka dai, Trump ɗin ya zama kashi biyu, ɗaya ya kan bayyana halayya daban a Tuwita ɗayan kuma ya kan faɗi abu daban a yayin jawabi daga fadarsa.