Wasu 'yan bindiga sun kashe mutum a birnin Kano

Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta kama mutum biyu da zargin kashe wani mai suna Isa Abubakar.

Kakakin rundunar a Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa, ya faɗa wa BBC cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren Asabar a kan Titin Gidan Zoo da ke ƙwaryar birnin.

Ya ƙara da cewa 'yan bindigar sun yi awon gaba da motar marigayi Alhaji Isa Abubakar mai shekara 50, wanda mazaunin unguwar Rijiyar Zaki ne.

"'Yan bindigar sun harbi mutumin sannan suka tafi da motarsa, kuma da jin harbin ne jami'anmu suka isa wurin, abin da ya sa maharan suka tsere cikin gaggawa" in ji Haruna Kiyawa.

"An garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano, inda a nan ne ya rasu."

Rahotanni sun ce mutumin ya yi yunƙurin hana su ƙwace masa motar a lokacin da miyagun suka nemi yin hakan, su kuma suka fito da shi da ƙarfin tsiya kuma suka harbe shi.

Haruna Kiyawa ya ce suna ci gaba da bincike kan mutum biyun da suka kama.

Hare-haren 'yan bindiga masu sacewa tare da garkuwa da mutane na ƙaruwa a yankin arewacin Najeriya.

Rahotanni daga Jihar Kaduna sun ce 'yan fashi sun kashe aƙalla mutum uku ranar Asabar a ƙauyen Kamaru da ke Ƙaramar Hukumar Kauru.

A makon da ya gabata ne rundunar sojan sama ta ƙasar ta ce ta ƙaddamar da wani shiri mai taken Operation Taimako Ya Zo da zummar zaƙulowa da kakkaɓe ayyukan 'yan fashin daji a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda mutane da dama suka mutu kuma aka yi garkuwa da wasu.