Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano: 'Yan bindiga sun sace wani ɗan kasuwa da ƙona motar ƴan sanda a Minjibir
Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace wani ɗan kasuwa tare da ƙone motar yan sanda, a garin Minjibir da ke jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewar ƴan bindigan sun kai harin ne a daren Talata, inda suka shiga gidajen maƙotan mutumin, kafin daga bisani su yi awon gaba ɗan kasuwan.
Wannan dai na zuwa ne ƙasa da kwanaki huɗu bayan wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane sun sace wata mata da ɗan da take raino a garin Falgore na Ƙaramar Hukumar Rogo mai maƙotaka da Kaduna da Katsina da ke fama da matsalar satar mutane.
Wani mazaunin garin na Minjibir da abin ya faru a kan idonsa, ya ce ƴan bindigar bayan sun iso garin, sai da suka fara shiga gidajen mutane suna neman attajirin sannan daga bisani suka ɗauke ɗan kasuwan a gidansa.
A cewarsa, a kan hanyar su ta fita suka yi ta ɗauki ba daɗi tsakanin su da yan'sanda.
Ya bayyana cewa tun da 'yan bindigan suka shiga garin ƙarfe ɗaya na dadare, ba su bar garin ba sai kusan huɗu da wani abu na dare suna ta harbe-harbe.
Ya kuma shaida wa BBC cewa 'yan bindigan sun haura mutum 50.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kwamishinan yan sanda na Kano Cp Habu Sani da kakakin rundunar ta Kano, DSP Abdullahi Kiyawa, sai dai ba su ce komai ba kan faruwar lamarin.
Rahotanni dai sun ce 'yan sanda daga sassa daban-daban na jihar ta Kano sun kawo ɗauki a lokacin da lamarin ke faruwa, inda suka yi ba ta kashi da yan bindigan, kuma 'yan bindigan sun samu nasarar ƙona motar ƴan sandan ɗaya bayan sun buɗe mata wuta.
Wannan al'amari ya fara jefa fargaba a zukatan mazauna birnin na Kano ganin yadda yan bindigar ke yiwa mutanen garin dauki daidai a kauyukan jahar.
Ƙaramar Hukumar Minjibir dai na maƙotaka da Gabasawa wadda ita ma a kwanakin baya aka sace ƙanin ministan aikin gona na Najeriya, Alhaji Sabo Nanono, amma daga bisani aka sako shi.
Haka zalika wasu da ake zargin ƴan bindigan ne sun ɗauke 'yar gidan dan majalisar dokokin Ɗambatta, a makonin da suka gabata , amma ita ma bayan biyan kuɗin fansa aka sako ta.
Da alama dai matsalar tsaro musamman satar mutane don neman kuɗin fansa na neman zama ruwan dare a akasarin jihohin arewa maso yammacin Najeriya, wani abin da ke ci gaba da jefa fargaba da tsoro a zukatan al'ummar da ke wannan yanki.