An kama mutumin da ake zargi da kashe wani yaro a Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da wani yaro tare da kashe shi bayan an ƙi biyansa kuɗin fansa.

Kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da BBC.

DSP Kiyawa ya ce tun a ranar 9 ga watan Nuwamba ne wani mutum mai suna Alhaji Kabiru ya kai musu ƙorafin cewa an yi garkuwa da ɗansa, an kuma nemi ya biya naira 1,300,000 da kuma katin waya na naira 20,000.

Nan da nan kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano ya bayar da umarnin a fara gudanar da bincike kan wannan lamari.

Bayan kwana 14 da samun rahoton, aka samu nasarar kama wanda ya aikata wannan laifi mai suna Anas Sa'idu matashi mai shekara 22 mazaunin ƙauyen Hayin Gwarmai da ke Kwanar Ɗangora a ƙaramar hukumar Bebeji, in ji kakakin rundunar 'yan sandan.

Ya yi bayanin yadda ya aikata lamarin da yadda ya kashe yaron da kuma kudin da ya nemi a biya shi a matsayin fansa.

"A yau ranar Juma'a 27/11/2020, kuma a yanzu haka muna cikin dajin muna haƙo gawar wannan yaro da aka kashe mai suna Tijjani Kabiru ɗan kimanin shekara 16, wadda ta ma gama lalacewa," a cewar DSP Kiyawa.

Sai dai ya musanta rahotanni da ke cewa mutumin da yas yi kisan yana da alaƙa ta jini da wanda ya kashe, yana cewa gari ne kawai ya haɗa su.

Ƙaruwar garkuwa da mutane

Da yake tsokaci kan ƙaruwar garkuwa da mutane a jihar, DSP Kiyawa ya ce a mafi yawan lokuta ana haɗa baki ne da makusanta ko kuma 'yan uwan wanda za a sata domin neman kuɗin, amma ba a fiye samun baƙi daga wani wuri ba suna aikata hakan.

"Akwai mu'amala mai kyau tsakanin rundunar 'yan sandan jihar Kano da kuma al'ummar gari a lokuta da yawa suna ba mu rahotannin baƙin fuska da kuma laifukan da suke aikatawa.

"Cikin kimanin shekara 11 an samu rahotannin garkuwa da mutane da muka samu ba su fi 10 ba zuwa 12, amma mun kama sama da mutum 117 da suke da hannu cikin haɗin bakin".

Sata da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa wani abu ne da ke ci gaba da addabar arewacin Najeriya, musamman a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna.

Ko a baya bayan na an sace mutane da dama ciki har da wasu malamai da dalibai da ma ma'aikatan Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.