An fara bincike kan zargin yi wa ɗalibi fyaɗe a makarantar Cocin Deeper Life

NIGERIA POLICE FORCE FACEBOOK

Asalin hoton, NIGERIA POLICE FORCE FACEBOOK

Bayanan hoto, 'Yan sandan jihar Akwa Ibom sun ce zuwa yanzu ba a kama kowa mutum guda da ake zargi kan wannan al'amari ba

Hukumomi a jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya sun ce suna gudanar da bincike kan zargin yi wa wani ɗalibi ɗan shekara goma sha ɗaya fyade a wata makarantar kwana mallakar wata coci.

Ana zargin manyan ɗalibai ne suka yi lalata da ƙaramin ɗalibin a sakandiren mai suna Deeper Life High school da ke Uyo babban birnin jihar. 

Batun dai ya karaɗe kafofin sada zumunta a 'yan kwanakin nan, inda mutane ke ta nuna kaɗuwa tare da kiran a ɗauki mataki.

Mahaifiyar yaron ce ta fara fito da maganar bainar jama'a, tana cewa ta ga alamomin raunuka a duburar yaron ɗan shekara goma sha ɗaya sakamakon fyaɗen da ake zargin manyan ɗalibai sun yi masa.

Ana dai zargin cewa wasu manyan ɗaliban makarantar ne suka yi ta lalata da shi bayan da aka sauya masa ɗakin kwana zuwa inda suke.

Rahotanni dai na cewa yanzu haka yaron na can yana jinya a asibiti.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar Akwa Ibom, ya shaida wa BBC cewa ana gudanar da bincike kan lamarin kuma duk wanda aka samu da hannu ta kowacce siga, za a gurfanar da shi gaban shari'ah. 

Sai dai, ya ce kawo yanzu ba a kai kama wani da ake zargi da hannu ba.

Rahotanni sun kuma ambato ma'ikatar ilmi ta jihar na cewa ita ma tana gudanar da bincike kan lamarin.

Makarantar Deeper Life High School wadda ta wata majami'ar pentecostal ce, hedikwatarta na birnin Legas amma tana da rassa a sassa daban-daban na Najeriya.

Tun farko, hukumomin majami'ar sun dakatar da shugabar makarantar ta birnin Uyo bayan ɓullar rahotannin fyaɗen.

A bayani na baya-bayan nan ta bidiyo a shafin Tuwitar Majami'ar, sakatariya Mrs Thelma Malaka, ta ce su a makaranta ba za su yi rufa-rufa ba kan duk wani zargin lalata, kuma suna goyon bayan bincken da hukumomi ke yi tare da fatan za a yi adalci.

Matsalar fyaɗe dai ta zama tamkar ruwan dare a Najeriya kuma wasu lokutan takan ritsa ne da ƙananan yara maza da mata.