Jerin ƙasashen da aka fara amfani da riga-kafin korona

Asalin hoton, Reuters
Riga-kafin annobar korona wanda aka ƙaddamar domin kare rayukan mutane an fara shi a ƙasashe da dama na duniya.
Tun bayan ɓullar annobar, sama da mutum miliyan 1.73 suka mutu a faɗin duniya inda mutum miliyan 78 suka kamu a hukumance a duniya.
A farkon watan Disamba ne Birtaniya ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta fara riga-kafin bayan an yi gwajinsa, daga baya kuma wasu ƙasashen suka bi sahun Birtaniyar.
Ga jerin ƙasashen da suka amince da riga-kafin da kuma fara yi wa jama'a
Birtaniya
A ranar 8 ga watan Disamba, Margaret Keenan, wata Baturiya mai shekara 90 ta zama ta farko da aka fara yi wa riga-kafin na Pfizer-BioNTech.
Sai dai jim kaɗan bayan da aka fara riga-kafin, sai Birtaniyar ta saka dokoki masu tsauri a ƙasar bayan ɓullar wani sabon nau'in cutar.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
An fara yin riga-kafin a Daular Larabawa a babban birnin ƙasar, Abu Dhabi, a ranar 14 ga watan Disamba.
Ƙasar ta amince da riga-kafin kamfanin Pfizer-BionNTech da kuma na kamfanin Chinar nan, Sinopharm domin amfani ga ilahirin ƴan ƙasar.
Amurka
Ita ma Amurka ta amince da amfani da riga-kafin kamfanin Pfizer inda aka fara yi wa wata malamar jinya mai suna Sandra Lindsay riga-kafin.
Sama da mutum miliyan guda aka yi wa wannan riga-kafin a Amurka tun bayan da aka ƙaddamar da shi.
Canada
Wata mata mai shekara 89 aka fara yi wa riga-kafin korona na kamfanin Pfizer a Canada a ranar 14 ga watan Disamba.
Ita ma ƙasar kamar maƙwafciyarta Amurka ta amince da riga-kafin kamfanin Moderna.
A yanzu dai Amurkar ta ƙaddamar da wani riga-kafin na biyu daga kamfanin Moderna.

Asalin hoton, Saudi Gazette
Saudiyya
Saudiyya ita ce ƙasar da wannan annoba ta fi yi wa illa a ƙasashen Larabawa inda sama da mutum 360,000 aka tabbatar da sun kamu, mutum 6,148 kuma suka mutu.
An fara yi wa ƴan ƙasar riga-kafi da allurar Pfizer-BioNTech a ranar 17 ga watan Disamba.
Isra'ila
An yi wa Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu riga-kafin korona a ranar 19 ga watan Disamba, inda ya ƙaddamar da riga-kafin.
An yi wa Netanyahu mai shekara 71, da ministan lafiyar ƙasar allurar riga-kafin Pfizer-BioNTech a asibitin Sheba na ƙasar inda aka nuna su kai tsaye a talabijin ana yi musu.
Qatar
Ƙasar Qatar ta ƙaddamar da riga-kafin korona kyauta bayan isowar kashi na farko na riga-kafin a ranar 22 ga watan Disamba
Mexico
Mexico ta ƙaddamar da shirinta na riga-kafi a ranar 24 ga watan Disamba, inda aka fara yi wa wata malamar jinya riga-kafin.
Mexico na daga cikin ƙasashen duniya da annobar ta fi yi wa illa.
Serbia da Kuwait da Chile da Costa Rica
Duka waɗannan ƙasashen sun ƙaddamar da riga-kafinsu na korona a ranar 24 ga watan Disamba.
Rasha
Rasha ta fara yi wa ƴan ƙasarta riga-kafin korona da riga-kafin da ta ƙirƙiro na Sputnik V.











