Christmas 2020: Abubuwa biyar da suka kamata ku sani game da bikin Kirsimeti

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Kirsimeti, rana ce da ake murna saboda zagayowar ranar haihuwar Yesu, kamar yadda yake a imanin duk wani mai bin addinin Kiristanci.
Duk da cewa an samu saɓani a kan cewa ranar 25 ga watan Disamba aka haife shi, wasu na cewa ba a wannan rana ba ce, amma mafiya rinjaye sun tafi cewa a wannan rana ce aka haifi Yesu al-Masihu.
Ranar da aka haifi Yesu
Waɗanda suka ce a ranar 25 ga watan Disamba wato watan 12 na shekarar aka haifi Yesu sun kafa hujja da nassi daga litattafai masu yawa.
A littafin Mathew sura ta biyu aya ta 11 da kuma littafin Luka sura ta biyu aya ta takwas zuwa ta 16, duka sun yi maganar wannan haihuwar Yesu a wannan rana ta 25.
Amma bikin Kirsimeti ya samo asali ne daga mala'iku ne suka fara yin shi, ta hanyar bushara da haihuwar Yesu, kamar yadda yake a cikin Luka sura ta biyu.
"Wannan yankin ƙasa kuwa akwai wasu bayin Allah makiyaya suna kiwon garken tumaki, sai wani mala'ikan ubangiji ya tsaya kusa da su da ɗaukakar ubangiji suka haskaka a kewayensu, har suka tsorata gaya, kamar yadda yazo a faɗar Ubangiji.
Rana ce ta farin ciki
Ko da Mala'ikun suka yi wannan albishirin, sai suka fara da rera waƙoƙi domin samun wanda zai zo wa duniya da salama, kamar yadda yake a aya ta 15 da ta 16 a littafin Luka.
"Idan mala'iku za su yi wannan murna su da ba sa zunubi, su wane ne ya fi kamata su yi murna sama da mutane masu zunubi a kullum", a cewar Rabaran Murtala Mati Ɗangora, mataimakin shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa reshen jihar Kano.
Don haka murna da farin ciki ya zama dole ga duk wani abin halitta da zai shiga ceton Yesu al-Masihu.

Asalin hoton, Getty Images
Ranar miƙa Kyautuka
Rana ce da ko ba ka iya ba da kyauta ba a matsayinka na mabiyi kuma Kirista ya kamata ka kwatanta ba da kyauta.
Dalili kuwa shi ne, a ranar ne aka yi wa duniya kyautar Yesu al-Masihu, wanda ya bayar da jininsa domin ceton zunubanmu.
"Mala'iku da masana taurari sun kwance jakunkunansu sun miƙa wa Yesu kyautuka na lubban da murru da kuma zinariya waɗanda su ne manyan abubuwa mafiya daraja a wancan lokacin don haka dole mu yi koyi da su," Rabaran Alex Garba Shekau Malamin wata coci a unguwar Bompai a Kano.
Ranar Sujjada ta ɗaukaka Ubangiji
A littafin Mathew, sura ta biyu aya ta 11, masana taurarin nan sun faɗi a gaban jaririn nan sun masa sujjada waɗanda su kuma abin koyi ne gare mu.
Don haka ranar ce ta yabon Allah da ɗaukaka sunan Ubangiji, rana ce da ake son ko wane kirista ya je ikilisiyya ya yi sujjada domin girmama ubangiji.
Wannan zai zama abin koyi ga mabiya, a kuma nemi a yi wa duniya baki daya afuwa kan zunuban bayi.
"Sai mala'ikun suka ce kada ku ji tsoro, albishir muka kawo muku na farin ciki, wanda zai zamana na dukkan mutane, domin yau an haifa muku mai ceto a birnin Dauda, wanda yake shi ne al-Masihu Ubangiji," kamar yadda yake a littafin Luka.
Rana ce ta salama ba a nuna banbanci a cikinta
Ba a son muzguna wa kowa Kirista ko ba Kirista ba, saboda ceto da Yesu ya zo da shi, a ranar ba a nuna bambanci.
Ba a son wani abu na ɓacin rai ya hana ka yin bushara da kowa, domin kuwa akwai haske da salama a zuwan wanda muke murnarsa.
Don haka a bikin da za a yi a wannan rana ba a cewa Kirista kawai za a bai wa kyauta ko kuma abincin da aka dafa domin ranar.











