Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɗaliban makarantar sakandaren Kankara sun isa Katsina
Ɗaliban makarantar sakandaren Ƙanƙara da suka kubuto daga hannun 'yan bindigar da suka sace su a makon jiya sun isa birnin Katsina da ke jihar ta Katsina a Najeriya.
Ɗaliban sun isa Katsina ne daga jihar Zamfara da ke maƙwabtaka bayan kwashe daren Alhamis a Gusau, babban birnin jihar.
A ranar ta Alhamis ne gwamnatin jihar Katsina ta ce an karɓo ɗaliban 344 kuma suna cikin ƙoshin lafiya.
Gwamnatin jihar Zamfara ce ta jagoranci karɓo ɗaliban tare da ƙungiyar Miyetti Allah ta ƙasa, a cewar Gwamna Bello Matawalle na jihar ta Zamfara.
Wakilin BBC Hausa, Khalifa Shehu Dokaji da yanzu haka yake Gidan Gwamnatin jihar ta Katsina, ya ce an shigar da ɗaliban ne a wasu manyan motocin bas-bas.
Ya ce za a sauke su a wani masauki inda za su yi wanka su ci abinci su kuma huta kafin daga bisani likitoci za su duba lafiyarsu.
Gwamnan jihar Katsina, wanda ya yi wa ɗaliban jawabi jim kaɗan bayan isarsu idan Gwamnati, ya bayyana matuƙar farin cikinsa bisa sakinsu.
Ya jinjina musu sannan ya yi kira a gare su da su ɗauki abin da ya faru da su a matsayin ƙaddara.
Yadda aka karɓo ɗaliban
Tawagar gwamnatin Zamfara ce ta karɓo yaran a hannun sojojin da suka fito da su daga dajin Tsafe da ke Zamfara da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Alhamis.
Sannan aka wuce da su barikin sojoji da ke birnin Gusau domin su rintsa inda daga bisani suka kama hanyar Katsina.
Gwamna Matawalle na Zamfara ya ce sun bi hanyar sulhu ne, wacce ta ba su nasarar ceto yaran ba tare da an kwashe lokaci mai tsawo ba.
Sannan ya tabbatar wa BBC cewa yara 344 aka sako, bayan samun jagorancin zaman sulhu ƙarƙashin shugaban Miyetti Allah na ƙasa.
"An yi zaman sulhu akalla sau uku kafin a kai ga cimma dai-daito ga sakin ɗaliban, da farko ya ci tura, haka zama na biyu amma a ƙarshe an yi nasara," in ji shi.
A hannun Boko Haram aka karbo yaran?
Gwamna Matawalle ya ce hannun Fulani ƴan bindiga aka karbo ɗaliban ba a a hannun Boko Haram ba.
Ya ce a zaman sulhun da suka yi da su sun gindaya musu wasu matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya wanda kuma aka alƙawarta za a sasanta.
Daga cikin ƙorafin Fulani akwai yadda ake kashe musu shanu da cin zarafinsu da ƴan banga ko ƙato da gora ke yi.
An biya kuɗin fansa?
Ƴan ƙasa da dama na sanya alamar tambaya kan yadda aka sako waɗannan ɗalibai, lura da dagar da aka sha a baya lokacin sace ƴan matan Chibok da Dapchi.
Akwai masu ganin abu ne mai wuya a sako wadannan ɗalibai haka kawai.
Sai dai bayanan da muka samu daga ɓangarorin gwamnatin Zamfarar da na Katsina na tabbatar da cewa ba a biya ko sisin kwabo ba a matsayin kuɗin fansa.
Kuma Gwamna Matawalle ya ce kawai an tattauna batutuwan da za su kare afkuwar irin wannan garkuwa ne a nan gaba, da kuma sauraron koken Fulanin da suka sace ɗaliban.
Gwamnan ya kuma danganta irin wannan matsaloli na tsaro da ake samu da rashin haɗin-kai, inda ya yi gargadi cewa aiki tare da sauraron koken juna ne kawai za su kuɓutar da Najeriya.