Google outage: Manhajojin Google na Gmail da Youtube sun daina aiki na ɗan lokaci

Asalin hoton, YouTube
Manhajojin Google da suka haɗa da YouTube da email da Docs sun tsaya cak, wanda abu ne da ba a saba gani ba, inda masu amfani da shafukan suka kasa amfani da su.
Manhajojin sun daina aiki ne na sama da mintuna 30 kafin suka dawo suna aiki, kuma hakan ya faru kafin karfe 12:00 na rana agogon Birtnaniya.
Masu amfani da manhajojin a faɗin duniya sun yi ta ƙorafin cewa suna samun tsaiko da manhajojin Gmail da Google Drive da Android Play Store da Maps da sauransu.
Sai dai shafin matambayi ba ya ɓata na Google da ake zuwa duba bayanai bai fuskanci wata matsala ba.
Tsaikon da manhajojin suka samu ya yi tasiri matuƙa ga miliyoyin mutanen da ke amfani da su waɗanda suka dogara kan Google ɗin domin yin ayyukansu na yau da kullum, musamman tura saƙon email da kuma kalanda.
Wannan matsalar ta shafi har wasu na'urorin Google da ke amfani da intanet, kamar sifiku na jin waƙa - inda wasu suka yi ƙorafi a kafefen sada zumunta cewa sun kasa kunnawa da kashe fitulun ɗakinsu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Haka kuma wasu da ke gudanar da wasan game na Pokémon Gosun sun yi ta ƙorafin cewa sun kasa bugawa.
A wata sanarwa da Google ɗin ya fitar, ya ce "Muna sane da matsalar da manhajar Gmail ke fuskanta da ke damun miliyoyin masu amfani da shi.
"Waɗanda lamarin ya shafa sun kasa shiga Gmail ɗinsu," in ji sanarwar, inda kalmar ta "Gmail" ɗin ta maye gurbin sauran manhajojin.
Google ɗin ya ce bai da tabbacin abin da ya jawo matsalar, an kuma nemi kamfanin na Google ɗin domin jin ta bakinsa, sai dai wani mai magana da yawun kamfanin ya ce su ma sun kasa ganin saƙon email ɗinsu a lokacin da lamarin ya faru.
Ba a cika samun irin waɗannan abubuwan ba, sai dai wasu matsaloli da aka samu na kamfanin sun jawo cikas ga masu amfani da manhajojin na Google a Amurka a Yunin 2019.











