Jihar Katsina: Mutanen garin da ke wuni a gida su kwana a maƙwabta don tsoron masu garkuwa da jama'a

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, AFP

"Duk jama'ar garin Sabuwa da zarar biyar da rabi zuwa shida na yamma ta yi za ka ga sun fara gudun hijira suna tsallakawa zuwa Hayin Gari da wasu ƙauyuka suna kwana saboda nan ne jami'an tsaro suke, domin haka ya fi tsaro a kan ƙaramar hukumar Sabuwa", in ji wani mazaunin garin da ke jhar Katsina ta arewacin Najeriya, yayin hira da BBC Hausa.

Ya ƙara da cewa "Da zarar an gama abinci sai dai a ƙulla a leda a tafi da shi, idan ka ga abin da ke faruwa sai ya ba ka mamaki da tausayi, za ka ga an kwashi 'ya'ya a hannu, wasu a goye, manya da yara suna barin gari kullum ta Allah," in ji shi.

Mutanen na tafiya wasu garuruwa da ke makwabtaka da Sabuwa da ke cikin jihar Katsina, zuwa yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a yammacin kowacce rana, saboda tsoron 'yan fashin daji da ke dirar musu kusan kowacce rana.

Wasu majiyoyi sun shaidawa BBC cewa satar mutane domin neman kuɗin fansa da fashi da makami sun ƙaru a garuruwa da ƙauyukan yankin, inda ko a wayewar garin ranar Laraba sai da 'yan fashin daji suka yi awon gaba da kimanin mutum goma ciki har da mai garin ƙauyen Gamji.

"Suka tsare mai garin suka ce su waye talakawa a cikin waɗanda idan aka buƙaci fansa ba za a samu ba, shi zai nuna ko su kashe shi, sai mai garin ya zaɓo talakawan suka dawo gida", a cewar mutumin.

Mutumin wanda ya nemi mu sakaye sunansa ya ce ba sa samun ɗaukin jami'an tsaro a duk lokacin da suka buƙaci tallafi daga gare su.

Shi kuwa wani ganau ɗin ya shaidawa BBC cewa su ma garuruwa irin su Sayau da Tashar Bawa,da Unguwar Na-Kaba da Dungun Mu'azu dukkaninsu a yankin Sabuwa sun fuskanci hare-haren yan fashin daji a baya bayan nan.

SP Gambi Isah, kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, ya shaida wa BBC Hausa cewa suna kokari wajen bin sahun mutanen Gamji da mai garinsu da aka sace, kuma yanzu haka suna wani sabon shiri don kawar da matsalar tsaro a yankin.

Ya ƙara da cewa: "An ɗauki mataki a kan yadda za a zo a killace wannan gari sannan a ɗauki matakan yaƙar waɗannan ƴan ta'adda ta yadda ba za su sake komawa garin ba."

Matsalar tsaro da satar mutane dai ta zama ruwan dare a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, musamman jihohin Zamfara da Katsina, inda ko a kwanan baya sai da rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin soji da zummar murƙushe masu garkuwa da mutane, sai dai har yanzu rahotannin satar jama'a da kai hare-hare na ci gaba da ƙaruwa.

Lu katsa alamar lasifika da ke ƙasa domin sauraren rahoton Muhtari Adamu Bawa:

Bayanan sautiMutanen garin da ke wuni a gida su kwana a maƙwabta saboda tsoron masu garkuwa