Boko Haram: Su wane ne sojojin haya da ake son Najeriya ta ɗauko?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau
A ranar Litinin ne Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya gabatar wa Shugaba Muhammadu Buhari buƙatu da yake ganin za su taimaka a yaƙi da Boko Haram, ciki har da ɗaukar sojojin haya.
Buƙatun na Gwamna Zulum sun biyo bayan harin rashin tausayi da Boko Haram ta kai wa manoma a garin Zabarmari na Borno ranar Asabar, inda ta yi musu yankan rago a kuma aka yi jana'izar mutum 43 a safiyar Lahadi.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce waɗanda aka kashe ɗin sun kai 110 amma rundunar sojojin Najeriya ta kafe cewa 43 ne.
An sha yaɗa cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta taɓa yin amfani da sojoijin haya a baya, sai dai BBC ba ta tabbatar da gaskiyar wannan labari ba.
Mun duba ko su wane ne sojojin haya da kuma irin ayyukan da suke gudanarwa a faɗin duniya.
Su wane ne sojojin haya?
Sojojin haya dakaru ne da ke yi wa wani kamfani aiki da ke samar da ayyukan tsaro ga wani mutum ko wata ƙasa a wani yanki na duniya domin a biya su.
Gwamnatocin kasashen duniya kan nemi yin aiki da irin waɗannan sojoji domin yin yaƙi kafaɗa da kafaɗa da sojojin ƙasar don yaƙar wata ƙasa ko kuma yayin yaƙi da wata ƙungiya ko 'yan tawaye a cikin ƙasar.
Sai dai akasarin kamfanonin ba sa son a riƙa kiransu da sojojin haya, sai dai a kira su 'yan kwangila.
Sean McFate, tsohon sojan Amurka kuma marabucin littafin Shadow War: A Tom Locke Novel, ya ce ita kanta kalmar "mercenary" wadda ke nufin sojan haya a Ingilishi ta samo asali ne daga kalmar "merces" wadda ke nufin "albashi" ko "biya" a harshen Latin.
A ina suke samun makamai?
Kamfanonin da ke aiwatar da irin waɗannan ayyuka kan je inda aka gayyace su da makamansu da dakaru, a cewar Barista Bulama Bukarti, wani lauya mai bincike kan matsalolin tsaro a Nahiyar Afirka.
Sai dai sukan yi amfani da wasu daga cikin kayan yaƙin ƙasar kamar jirage, in ji shi.
Su wane ne ke amfani da sojojin haya?
An shafe shekaru ɗaruruwa ana amfani da sojojin haya a yaƙe-yaƙen da aka fafata a duniya baki ɗaya, sai dai ƙasashe da dama sun haramta wa 'yan ƙasashensu shiga irin waɗannan rundunoni.
Amma Amurka ta sake farfaɗo da ayyukan sojojin haya bayan yaƙin cacar baki na shekarun 1980 tsakanin da tsohuwar Tarayyar Soviet ƙarƙashin jagorancin Rasha.
Cikin wata maƙala da ya rubuta mai taken "Abu Goma da Ba Ku Sani Ba Game da Sojojin Haya" a 2016, Sean McFate ya ce ba wai ƙasashen da ke fama da rashin tsaro ne suka farfaɗo da ayyukan sojojin haya ba, hasali ma manyan ƙasashen duniya ne da suka fi kowa ƙarfin soja.
Misali, a shekarar 2010 Amurka ta ware dala biliyan 366 domin ɗaukar sojojin haya - ninki biyar kenan na abin da Birtaniya ta ware wa ɓangaren tsaronta a kasafin kuɗi.
Me ya sa Amurka ke amfani da sojojin haya duk da ƙarfin sojanta?
Babu tantama cewa Amurka ce ƙasa wadda ke da rundunar soja mafi ƙarfi a duniya, amma duk da haka ƙasar ce kan gaba a harkokin sojan haya.
Babban dalilin da ya sa ƙasar ke amfani da sojojin haya shi ne gwamnati ba za ta iya ɗaukar yawan adadin sojojin da take buƙata ba domin ƙaddamar da yaƙi da take yi a faɗin duniya, a cewar Sean McFate.
Kashi 50 cikin 100 na sojojin Amurka da ke yaƙi a Iraƙi na haya ne, kashi 70 ne Afghanistan, yayin da kuma kashi 10 kawai ta ɗauka a Yaƙin Duniya na Biyu.
Daga ina ake samo sojojin haya?
Sojojin haya kamar sauran kamfanoni ne na duniya, sukan ɗauki ma'akata daga kowane lungu da saƙo na duniya.
Kazalika, kamfanonin kan biya ma'aikatan albashi daban-daban. Haka nan, sun fi son su samu aiki me yawa a kuɗi kaɗan.
Sean McFate ya ce akasarin mayaƙan haya da AMurkar ke amfani da su ba 'yan ƙasar ba ne, kuma ma an fi kashe su sama da sojojin ƙasar a yaƙe-yaƙe baya-bayan nan.
Ƙasashen da sojojin haya suka fafata yaƙi
Wani ɗan kwangilar soja a Afirka ta Kudu kuma shugaban kamfanin Executive Outcome mai suna Eeben Barlow ya faɗa wa kafar watsa labarai ta Aljazeera cewa kamfaninsa mai samar da sojojin haya ya yi ayyuka a ƙasashen Afirka da dama.
Ya ce gwamnatin Angola ta ba su aikin horar da sojojinta da kuma taimakawa wurin yaƙar 'yan tawayen Unita a ƙasar amma daga bisani Majalisar Ɗinkin Duniya ta matsa wa ƙasar lamba sai da ta daina amfani da su.
A ƙasar Saliyo ma wato Sierra Leone sun fafata, inda suka taya gwamnatin ƙasar yaƙi kafin Bankin Duniya da asusun bayar da lamuni na IMF su matsa wa gwamnati fita daga sha'aninsu.
Wani rahoto da jaridar New York Times ta wallafa a watan Nuwamban 2015 ya bankaɗo yadda ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta hayi sojoji daga ƙasar Colombia a asirce domin fafatawa a yaƙin Yemen.
Rahoton ya ce adadin sojojin ya kai 450 a yaƙin da Saudiyya ke jagorantar ƙawayenta a Yemen tun daga 2014 zuwa yanzu, inda ƙasashen ke yaƙar ƙungiyar Huthi mai alaƙa da ƙasar Iran.
Ƙawararre kan harkokin soja Sean McFate ya yi iƙirarin cewa ita ma Najeriya ta taɓa yin amfani da sojojin haya a yaƙi da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi.
Ya ce Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya hayi sojoji domin yin yaƙi a gabashin Ukraine.
Haka nan sojojin haya na fafatawa a yaƙe-yaƙe a ƙasashen Syria da Iraƙi da Afghanistan da Somalia.











