Ta yaya Boko Haram suke aiki da fasahar wallafa bidiyo a tsakiyar daji?

Abubakar Shekau

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Abubakar Shekau ya sha fitowa a bidiyo yana barazana da kuma ɗaukar alhakin kai hare-hare

Tun bayan da ayyukan yan ta'adda ya yi kamari a wasu sassan duniya cikin gwamman shekarun da suka gabata da kuma yadda intanet ke ci gaba da yaduwa, ƙungiyoyin ta'addanci daba-daban su ma suke cin moriyar intanet din ta hanyar aike wa al'umma da sakonninsu a duk lokacin da suka so.

Kungiyoyi irin su al-Qaeda da al-Shabab da IS da ISWAP da Boko Haram da dai sauransu, waɗanda yawancinsu ke ayyukansu daga cikin dazuzzuka ko wurare masu surkuki, kan yi bidiyo su kuma yi amfani da intanet wajen yaɗa su.

Kungiyar Boko Haram da ta samo asali daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya alal misali, an yi amannar tana kitsa ayyukanta ne daga dajin Sambisa, wajen da za a iya cewa ba lallai a samu karfin intanet din da za a aika ko ɗora bidiyo masu nauyi irin wanda kungiyar ke yi ba a duk lokacin ta bushi iskar isar da saƙo.

A baya-bayan nan ma Boko Haram ta fitar da sakon bidiyo bayan da mayakanta suka yi wa manoman shinkafa sama da 70 kisan gilla a ƙauyen Zabarmari da ke jihar Borno, kuma kwanaki kaɗan bayan hakan sai ga bidiyon sakon ƙungiyar ya bayyana.

Hakan ya sake bujiro da tambayar da dama ta daɗe tana damun mutane kan ta yaya suke haɗa bidiyon ne? A ina suke samun intanet ɗin da suke amfani da shi wajen ɗora bidiyon?

Don jin wadannan amsoshi da ma wasu, BBC Hausa ta tuntubi wani mai bincike kan harkokin tsaro a Afirka Barista Bulama Bukarti.

Barista Bukarti wanda ya yi wani bincike a shekarar da ta gabata kan wannan lamari ya ce ya gano cewa mayaƙan Boko Haram suna da kyamarori da manyan wayoyi masu iya daukar hoto mai kyau.

"Da waɗannan wayoyi ne suke ɗaukar hotunan hare-haren da suke kai wa da kuma hotunan kansu da suke yaɗawa. Sannan kuma suna da kwamfutocin hannu, waɗanda da su suke amfani wajen harhaɗa hotunan da tace su.

"Sannan idan suka tashi yaɗa hotunan da bidiyon, suna yin hakan ne ta hanyar amfani da Whatsapp da Telegram", in ji Bukarti.

Mai binciken ya ce ta bangaren kungiyar IS reshen Afirka Ta Yamma kuma wato ISWAP, ya gano cewa suna da zaurukan WhatsApp akalla 50 a bara, kuma suna bude da yawa ne saboda idan kamfanonin manhajojin suka gane masu amfani da zaurukan sai su rufe.

''To saboda kar a rufe musu su rasa wajen tura bayanai, sai su buɗe da yawa ta yadda idan aka rufe ɗaya to suna da wani. Haka ma suna da na Telegram da yawa.

"Sannan kuma idan aka ruɗe musu sai su je Telegram su yada bayani kan sunan sabon zauren Whatsapp din da suka rufe bayan rufe tsohon. Don haka an rufe musu wasu suna sake bude wasu.

"Wani lokaci idan aka rufe ɗaya sai su sake buɗe 10," a cewar Barista Bukarti.

To a ina suke samun intanet kuma?

Barista Bukarti ya ce a iya bincike da fahimtarsa ya gano cewa babu intanet a yankin da shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yake zaune.

"Amma yadda suke, shi ne sai a ɗauki bayanansa a bidiyo a inda yake ɗin, sannan sai su gyara, daga nan sai su tura wakilai su hau abin hawa su lalaba kusa da gari, yawanci su kan je kusa da garin Maiduguri ne don su samu karfin intanet.

Mai binciken ya ci gaba da cewa ya taɓa samun wasu bayanansu da aka taɓa naɗa da suka ce akwai lokutan da suke shan wahalar samun intanet ta yadda su kan shafe kwanaki suna zauwa gefen gari amma sai intanet ɗin ya ƙi samuwa.

Sannan ya bayyana cewa waɗannan mayaƙa na Boko Haram ba da ka suke waɗannan ayyuka ba, don akwai masu ilimin zamani da na sanin kwamfuta da dama a cikinsu.

"Suna karance-karance kan yadda za su bi su yaɗa saƙonninsu ba tare da an gane wa yake yada su ba. Sannan daga jerin shugabannin zaurukan Whatsapp din su za a ga cewa wasu ma lambobin ba na Najeriya ba ne na Sudan ne ko Nijar. Na ma taba ganin lambar Libiya.

"Hakan kan sa a kasa gane wa yake yi ma kuma ba su yin kiran waya sun fi son Whatsapp saboda ya fi tsaro."

Sauran mambobin da suke cikin zaurukan WhatsApp sun haɗa da wasu daga Mali da Burkina Faso, da sauran kasashe.

Barista Bukarti ya ce: "Idan ba a manta ba akwai hare-haren da aka kai Mali da Burkina Faso amma ISWAP ta yi ikirarin ita ta kai saboda a cewarsu sun fadada cibiyonsu a yankin kudu da Hamadar Sahara.

"Kuma su ma hotuna da bidiyon hare-haren da suke kai wa suna rarraba su ne ta zaurukan Whatsapp da su kan bude, kuma akwai mambobi ƴan Najeriya da Larabwa na Iraƙi da Syria a ciki da suke ɗauka su ma suna rarrabawa," a cewar mai binciken.

A ina suke samun komfutoci da manyan wayoyi?

Shugaban kungiyar BH Abubakar Shekau

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Boko Haram ta fara kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2009

Dole duk mai nazari ya yi wannan tambayar cewa a ina ƴan ta'addan ke samun kayayyakin fasahar da suke amfani da su ta wajen ɗauka da yaɗa bidiyonsu.

Sai dai a ganin Barista Bukarti suna samu ne ta wajen ƙwacen da suke yi a yayin da suka kai hare-harensu.

"Mun san cewa a farko-farkon fara yaƙin sun yi ta kai hare-hare a bankuna da makarantu da ma'aikatun gwamnati, to ta yiwu, wasu daga cikin komfutoci da wayoyin sun sato su ne a waɗannan wurare.

"Kuma mun san a yanzu da suka tare hanyoyi suna ƙwace suna kuma shiga ƙauyuka, yawanci idan suka tare mutane ko suka halaka su ko suka sace, to su kan yi dace da samun waɗannan kayayyakin a tare da su," in ji Bukarti.

Ya ƙara da cewa ko a baya-bayan nan ya yi hira da wata da ta tsallake rijiya da baya bayan da mayaƙan Boko Haram suka tare wata mota da take ciki a hanya.

"Sai dai ta yi barka ba su kashe ta ko sace ta ba amma sun ƙwace duk wayoyinsu da komfutocin sun tafi da su.

"To ta nan ne suke samun wayoyi na zamani da komfutoci suna amfani da su wajen yaɗa bayanan da suke so," in ji Bukarti.