Coronavirus: Ƙasashe masu arziki 'suna ɓoye riga-kafin cutar korona'

Ƙasashe masu arziki na ɓoye riga-kafin cutar korona yayin da mutanen da ke ƙasashe matalauta za su iya rasa wa, kamar yadda gamayyar masu fafutuka suka yi gargaɗi.

Gamayyar ƙungiyoyi ta The People's Vaccine Alliance ta ce a kusan ƙasashe 70 marasa ƙarfi mutum ɗaya cikin 10 ne kawai za su iya yi wa riga-kafi.

Wannan kuma duk da alƙawalin da aka yi cewar za a samar da kashi 64 na rigakafin Oxford-AstraZeneca ga ƙasashe masu tasowa.

Ana ɗaukar matakai domin tabbatar da adalci wajen raba rigakafin a sassan duniya.

Alƙawarin riga-kafin wanda ake kira Covax, ya samu nasarar samar da riga-kafin miliyan 700 da za a rarraba tsakanin ƙasashe 92 masu ƙaramin ƙarfi da suka buƙata.

Amma duk da wannan tsarin, People's Vaccine Alliance - gamayyar ƙungiyoyi da suka haɗa har da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International da Oxfam da Global Justice Now - ta ce babu wadatar rigakafin da za a rarraba, kuma ya kamata kamfanonin samar da maganin su bayyana fasaharsu domin samar da riga-kafin da yawa.

Bincikensu ya gano cewa manyan ƙasashe sun samar da rigakafin da dama domin ƴan ƙasarsu, idan har an amince a yi amfani da su.

Misali Canada, ta yi odar rigakafin domin kare ɗan Canada kusan sau biyar, kamar yadda ƙungiyar ta yi iƙirari.

Kuma manyan ƙasashe waɗanda ba su wuce kashi 14 na yawan al'ummar duniya ba, sun samar da kashi 53 na riga-kafin zuwa yanzu

"Bai kamata a hana wani damar damun rigakafin ba, bisa dalilin yadda ƙasar take ko kuma kuɗin da take da su," a cewar Anna Marriot, ta ƙungiyar Oxfam

"Sai idan abubuwa sun sauya, amma biliyoyin mutane a sassan duniya ba za su samu riga-kafin korona a tsawon shekaru masu zuwa."

Gamayyar ta yi kira ga kamfafofin magani da ke aiki kan samar da riga-kafin korona su bayyana fasaharsu ga kowa domin samar da biliyoyin riga-kafin.

Za a iya samar da wannan ta hanyar fasahar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, kamar yadda suka bayyana.

AstraZeneca, kamfanin da ya samar da rigakafin korona tare da jami'ar Oxford, ya yi alƙawarin samar da riga-kafin ga ƙasashe masu tasowa.

Ya fi sauki fiye da saura kuma za a iya ajiye shi cikin firjin, wanda hakan zai sauƙaƙa wajen rarraba shi zuwa sassan duniya.

Amma masu fafutika sun ce kamfani ɗaya ba zai iya samar da rigakafin ba a duniya.

Riga-kafin haɗin guiwar Pfizer da BioNTech tuni aka amince da shi a Birtaniya, kuma waɗanda suka fi fuskantar hatsari su aka fara yi wa riga-kafin a wannan makon.

Da Alama kuma zai samu amincewa daga hukumomi a Amurka da Turai, wanda hakan ke nufin za a iya ɗaukar lokaci kafin a raba shi zuwa ƙananan ƙasashe.

Sauran riga-kafin guda biyu, Moderna da Oxford-AstraZeneca, suna jiran amincewar hukumomi.

Riga-kafin Rasha, Sputnik, ya sanar da samun nasara a sakamakon gwajin maganin, kuma wasu rigakafin huɗu na jiran sakamakon gwajin tabbatar da ingancinsu.