Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Maurice Kamto: An kawar da jami'an tsaro daga gidan madugun adawar Kamaru
Gwamnatin Kamaru ta kawar da jami'an tsaron da ta girke a ƙofar gidan babban ɗan adawa Maurice Kamto, tun ranar 20 ga watan Satumbar shekarar 2020.
Girke jami'an tsaron da gwamnati ta yi tsawon sama da wata biyu ya biyo bayan aniyar da kakakin jam'iyyar MRC ya nuna na yin zanga-zangar lumana tare da magoya bayansa a ranar 22 ga watan Satumbar domin nuna abin da ya kira rashin amincewa da nuna halin-ko-in-kula da gwamnati ta yi game da rikicin yankin renon Ingila.
Hukumomi sun ba wa jami'an tsaro na 'yan sanda da jandarma da suke zaman kasko a ƙofar shiga gidan Maurice Kamto umarnin barin gidan.
Wannan ya nuna cewa daga yanzu yana da damar karɓar baƙuncin dukkanin wadanda suke da buƙata su gana da shi, ko kuma ya gana da su, saɓanin abin da ya wakana a duk tsawon kwanaki 75 da ya deba yana zaman talala duk da cewa kuma ba a sanar da shi haka a hukumance ba.
Shugaban lauyoyin Mourice Kamto, Me Hyppolyte Melim ya rubuta a shafinsu na lauyoyin da suke kare Maurice Kamto cewa sun yi gwagwarmaya na tsawon kwanaki 75 ba tare da sun fahimci muhimmancin girke jami'an tsaro da aka yi a gaban gidan Maurice Kamto ba.
Jami'an tsaro sun naɗe taburmansu ne jim kaɗan bayan wata sanarwar da kakakin gwamnati Minista Rene Emmanuel Sadi, ya fitar yana yabawa da yadda zaɓukan kansalolin larduna suka gudana ba tare da an fuskanci wata babbar mushkila ba.
Duk da cewa wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da jam'iyyun siyasa suna yin barazana game da yadda zaɓukan suka gudana an bayyana yadda za a daɗa ƙarfafa matakan tsaro domin tanƙwara wuyan duk wani yunkurin yin bore, da take doka da kakakin jam'iyyar MRC Maurice Kamto zai yi.
Kazalika Minista Rene Emmanuel Sadi, ya bayyana cewa an yi sassauci ga wasu magoya bayan jam'iyyar MRC da suke tsare a gidan yari lamarin da ya kai ga sun sake samun 'yancinsu na kai kawo.
Laifin da ake zargin Maurice Kamto da aikatawa da ya kai ga ya yi zaman ɗaurin talala shine kira domin a yi bore da hukumomi suka ce ya yi da magoya bayansa saboda nuna rashin gamsuwa da yadda ake gudanar da zaɓen kansalolin larduna.