Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙalubalen da za a fuskanta idan tattalin arzikin Najeriya ya ci gaba da taɓarɓarewa
Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce koma-bayan da tattalin arzikin ƙasar ya fada a cikin karo na biyu a shekara biyar bai zo musu da mamaki ba.
Tattalin arziƙin Najeriya ya ragu da kashi 3.62 cikin 100 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2020, a cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasar, National Bureau of Statistics (NBS).
Ɗaya daga cikin masana tattalin arziƙi a Najeriya, Farfesa Mustafa Mukhtar, Malami a sashen nazarin harkar tattalin arzikin ƙasa na jami'ar Bayero ta Kano, ya shaida wa BBC cewa, "wannan batu ba abin mamaki bane domin shi da ma tattalin arzikin ƙasa kamar igiyar ruwa ne, wata rana ya yi sama wata rana kuma ya yi ƙasa" a cewarsa.
Farfesan ya ce akwai matsalolin da suka janyo Najeriya ta sake faɗawa cikin matsalar tattalin arziki, ciki kuwa har da ɓurɓushin matsalar da cutar korona ta haifar wanda ya sa aka rufe wasu ɓangarori na tattalin arzikin ƙasa musamman harkar masana'antu a inda kasuwanci ya samu naƙasu.
Masanin tattalin arzikin ya ce: "Abu na biyu wanda yana daga cikin matsalolin da suka jefa tattalin arzikin Najeriya cikin mawuyacin yanayi shi ne matsalar da aka samu a ɓangaren sayar da man fetur a kasuwar duniya, inda farshin man ya ke kwan-gaba kwan-baya kuma har yanzu bai daidaita ba."
Ya ce sanin kowa ne tattalin arzikin Najeriya yawancinsa ya ta'allaƙa ne a kan farashi da kuma rarar kuɗi da ake samu idan an sayar da ɗanyen man fetir.
Farfesa Mustapha ya ce: "Faduwar farashin man fetir da aka samu a kasuwar duniya ta sa Najeriya ba ta samun kuɗaɗen shiga isassu wanda hakan ya janyo tattalin arzikin ƙasar ya ja baya".
Masanin tattalin arzikin ƙasar ya ce idan aka samu matsala a ɓangaren man fetur da masana'anta, to dole ne ɓangaren cinikayya da hada-hadar kuɗi da inshora da kuma harkar noma su samu naƙasu.
Ya ce kasancewar duk wadannan ɓangarorin sun samu matsala shi ya sa tattalin arzikin Najeriya ma ya samu matsala.
'Za a shiga mawuyacin hali'
Farfesa Mustafa Mukhtar ya ce idan har aka ci gaba a haka, to ko shakka babu za a shiga mawuyacin yanayi musamman gwamnatin Najeriya da gwamnatocin jihohi da kuma na ƙananan hukumomi.
Masanin tattalin arzikin ya ce "gwamnatoci a matakan ukun ba za su iya taɓuka komai ba musamman waɗanda aka saka a cikin kasafin kuɗi, don haka dole sai a samo mafita idan an so komai ya tafi yadda ake so.
Dangane da abubuwan da ya kamata ayi dan a fita daga wannan koma baya da tattalin arzikin Najeriya ya shiga, farfesan ya ce, dole ne sai gwamnatin tarayyar ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da babban bankin ƙasa don a ƙara samar da ayyukan yi, a samar da jari, sannan a taimakawa ƙananan da manyan masana'antu, a bunƙasa harkar kasuwancin sannan kuma a samar da ababan more rayuwa.
Ya ce kuma dole ne a bunƙasa harkar noma don abubuwa su tafi yadda ake so.
Ƙarin bayani
Bankin duniya ya ce wannan shi ne koma bayan tattalin arziki mafi muni da Najeriya ta tsinci kanta ciki a cikin shekara 36.
Ƙasa dai na shiga karayar tattalin arziƙi idan adadin arziƙin da take samarwa a ƙasar ya ragu cikin wata shida a jere ba tare da ya farfaɗo ba.
A daidai lokacin da Najeriyar ke ƙara shiga halin karayar tattalin arziƙi, darajar kuɗin Najeriya ta ƙara raguwa idan aka kwatanta da na sauran ƙasashe da ke gogayya da naira a kasuwannin duniya.