Kotu ta bayar da belin wanda ya haɗa bidiyon 'auren Buhari da Sadiya' kan miliyan ɗaya

Shugaba Buhari da Sadiya Farouk

Asalin hoton, Presidency

Wata kotun Majistare a Kano ta bayar da belin mutumin da aka kama bisa zarginsa da haɗa bidiyon auren shugaba Buhari da ministarsa Sadiya Farouq.

An gurfanar da ɗan Najeriya gaban kotu, bayan kama shi tun a watan Janairu bisa zarginsa da haɗa bidiyo na bogi da ke nuna Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya auri Minista Sadiya Farouq.

Hukumar tsaro ta DSS ce ta kama Kabiru Mohammed tun a watan Janairu, inda sai a ranar Talata ne aka kai shi kotu.

Hukumar tsaro ta farin kayan ta bayyana cewa wanda ake zargin, ya amsa laifin haɗa bidiyon na bogi.

An gurfanar da Mohammad Kabir a gaban Kotun Majistare da ke Normansland da ke birnin Kano.

Kotun dai ta bayar da belinsa da ake zargin kan kudi naira miliyan daya duk da cewa hukumar DSS ɗin ta buƙaci kotun da kada ta bayar da belin wanda ake zargin sai ta kammala bincike tare da neman shawara daga ma'aikatar shari'a ta jihar Kano.

Kotun ta ƙeƙashe ƙasa ta bayar da belin Kabiru bayan da lauyansa ya gabatar da hujjojin da suka nuna cewa laifin da ya yi za a iya bayar da belinsa.

Sauran sharuɗɗan belin sun haɗa da kawo mutum biyu da za su tsaya wa Kabiru waɗanda ko dai su kasance shugaba ko sakatare na ƙungiyar ƴan kasuwar singa, inda wanda ake ƙarar ke sana'ar sayar da shinkafa, sannan na biyun ya kasance ma'aikacin gwamnati da ke mataki na 14.

Sannan hukumar tsaro ta farin kaya ta gano gidan da wanda ake ƙara ke zaune tare da tabbatar da cewar zai ringa kai kansa gaban hukumar tsaron ta farin kaya.

An bayyana wa kotun cewa bidiyon ya ɓata sunan waɗanda aka yi domin su kuma ya jawo matsaloli ga iyalansu.

A yanzu dai an ɗage sauraren ƙarar zuwa 5 ga watan Fabrairun 2021.

Tun a cikin watan Agustan shekarar 2019 ne bidiyon auren bogin na Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da Ministar jin ƙan al'umma ta ƙasar, Sadiya Faruk ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta.