Masu ikirarin jihadi 'sun fille wa fiye da mutum 50 kawuna' a Mozambique

In this file photo taken on August 24, 2019 The remains of a burned and destroyed home is seen in the recently attacked village of Aldeia da Paz outside Macomia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dubun-dubatar mutane ne suka tsare daga gidajensu, saboda an lalata musu su a rikicin da aka shafe shekara uku ana yi

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin ƙasar Mozambique ta ce masu ikirarin jihadi sun fille wa fiye da mutum 50 kawuna.

Mayaƙan sun mayar da wani filin ƙwallo da ke wani ƙauye zuwa ''dandalin kashe mutane," inda suke yin gunduwa-gunduwa da jikin mutane, kamar yadda wasu rahotannin suka ce.

Mutane da dama ne aka kuma fille wa kai a wani ƙauyen daban, kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta ruwaito.

Fille kawunan shi ne al'amari na baya-bayan nan a wasu jerin munanan hare-haren da mayaƙan suka kai a yankin da ke da arziƙin iskar gas na Cabo Delgado tun a shekarar 2017.

An kashe kusan mutum 2,000 sannan aka raba 430,000 da muhallansu a rikicin da ake yi a yankin Musulmai suka fi yawa.

Ana alaƙanta mayaƙan da ƙungiyar IS, inda take samar musu wurin zama a kudancin Afirka.

Ƙungiyar ta jawo talauci da rashin ayyukan yi inda take shigar da matsa cikin aƙidarsu da ƙoƙarin kafa ''Daular Musulunci'' a yankin kamar yadda suke ikirari.

Mutanen yankin da dama suna ƙorafin cewa ba sa wani amfana sosai da arzikin iskar gas da ke wajen.

Map of Mozambique

Wakilin BBC Jose Tembe ya ruwaito daga babban birnin Maputo cewa, al'amarin na baya-bayan nan mai yiwuwa shi ne mafi muni da mayaƙan suka taɓa kai wa.

Mutane da dama sun kaɗu, suna kira ga a warware matsalar cikin lumana, kamar yadda ya ce.

Ƴan bindigar sun yi kabbara suna "Allahu Akbar" wato "Allah Mai Girma", suna harba bindiga sannan suka dinga ƙona gidaje a lokacin da suka kai hari ƙauyen Nanjaba a ranar Juma'a da daddare, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Mozambique ya ruwaito waɗanda suka tsira suna faɗa.

An fille wa mutum biyu kawuna kuma an sace mata da dama, kamfanin dillancin labaran ya ƙara da cewa.

Wata ƙungiyar mayaƙan daban kuma ta kai wani mummunan harin ƙauyen Muatide, inda suka fille kawunan fiye da mutum 50, in ji kamfanin.

An kamo mutanen ƙauyukan da suka gudu, aka kai su filin ƙwallo inda aka fille musu kawuna tare da yin gunduwa-gunduwa da jikinsu a wani bala'i da ya faru daga ranar Juma'a har zuwa daren Lahadi, in ji wata kafar yaɗa labarai mai zaman kanta Pinnancle News.

Gwamnatin Mozambique ta nemi taimakon ƙasashen duniya don magance ta'addancin, tana mai cewa dakarunta na buƙatar horo na musamman.

A watan Afrilu, an fille wa fiye da mutum 50 kawuna ko kuma an harbe wasu har lahira a wani hari da aka kai ƙauye na Cabo Delgado, kuma a farkon wannan watan ma an sake fille kawunan wasu mutum tara a wannan yankin.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun ce dakarun tsaron Mozabique ma sun aikata cin zarafin ɗan adam da suka haɗa da kama mutane ba bisa ƙa'ida ba, da azabtarwa da kisa a lokacin da ake ƙaddamar da wasu hare-haren yaƙi da ta'addanci.