Yadda yawan gina rijiyar burtsatse ke haifar da sauyin yanayi a Najeriya

Asalin hoton, WaterAid
Wani rahoto da kungiyar Water Aid, mai yunƙurin ganin an samar da tsaftataccen ruwa ta fitar ya yi kira da a gaggauta kare ruwan da ke ƙarƙashin ƙasa, wanda ta ce babbar kariya ce ga barazanar sauyin yanayi.
Rahoton ya ce ana samun ruwa a ƙarƙashin ƙasa a ko ina kuma ya ƙunshi kashi 30 na samun tsabtataccen ruwan sha a duniya, kuma yana bayar da kariyar da ake buƙata sosai game da tasirin sauyin yanayi.
WaterAid ta ce tatsar ruwan ƙarƙashin ƙasa ya kasance albarkatun ƙasa da aka fi haƙowa a duniya tun 1940 da aka samu bunƙasar masa'anatu.
Ƙungiyar ta ce idan har ba a kare ruwan ƙarƙashin ƙasa ba, al'umomi da dama za su fuskanci matsalar rashin wadataccen ruwan sha a nan gaba, saboda za a iya rasa hanyoyin da ake samun ruwan saboda sauyin yanayi.
Rahoton ƙungiyar ya ce ruwan karkashin kasa yana ba da kariyar da ake buƙata sosai game da tasirin sauyin yanayi sauyin ruwa da inganci a ɓangarori da dama na duniya.
"Rashin ingantaccen tsarin kare manufofin ruwan karkashin kasa ya sa ana wuce gona da iri da kuma haifar da matsaloli ga samun wadatuwar ruwan a nan gaba," a cewar babbar daraktar ƙungiyar a Najeriya Mrs Oluseyi Abdul Malik.
Ta kuma yi gargadin cewa matsalar rashin bibiya da kuma yadda ake matuƙar ɓarnatar da ruwan ƙarƙashin ƙasa, na jefa miliyoyin rayuka cikin hatsari a duniya.

Ina matsalar take?
Mafi yawanci an koma dogaro ne da gina rijiyoyin ruwa na burtsatse da kuma na tuƙa-tuƙa musamman a ƙasashen Afirka da yankunan Asiya a matsayin hanyar samun ruwa.
Sauyin yanayi ya yi tasiri sosai ga rashin wadatar ruwa ta hanyar ƙafewar wuraren da al'umma ke dogaro da su wajen samun ruwan.
Rahoton WaterAid ya ce ya gano rashin kula da ɗaukar matakan da suka dace kan yadda ake tonon ruwan a ƙarƙashin ƙasa a ƙasashe kamar Najeriya da Bangladesh da Indiya.
Wannan kuma babbar barazana ce ga matsalar sauyin yanayi yayin da kuma yawan al'umma ke ci gaba da ƙaruwa.
Duk da akwai dokoki game da gina rijiyoyin burtsatse kamar a Najeriya, amma kuma gwamnatoci ba su damu da sa ido ba da kuma yawan burtsatsen da ya kamata a gina a unguwa.
Rahoton ƙungiyar WaterAid ya ce a Najeriya akwai sama da mutum miliyan 60 da ke fama da rashin ruwan sha.
Binciken da aka yi a kasashe biyar da kungiyar ke aiki cikinsu, ya ce akwai mutum sama da miliyan 165 da ba sa da hanyar samun tsaftataccen ruwan sha a gidansu.
Ya ce wannan ɓoyayyiyar albarkar ƙasa, na samar da wani muhimmin shamaki ga matsalar sauyin yanayi

Yawan gina rijiyar burtsatse barazana ne
A cewar rahoton, akwai fargaba game da barazanar da ke fuskantar ruwan ƙarƙashin ƙasa a faɗin duniya, wanda miliyoyin mutane suka dogara da shi wajen samun ruwan buƙatun yau da kullum.
Ya kara da cewa matukar gwamnatoci da masu ruwa da tsaki a fadin duniya ba su mayar da hankali kan tattala ruwan da ke cikin kasa ba al'ummomi da yawa za su faɗa cikin mawuyacin hali.
Amma hakan zai fi tasiri ne a lokacin da matsalar sauyin yanayi za ta gurɓata ruwan da ke karkashin ƙasar.
Binciken ya jero kasashe irin su Bangladesh da Ghana da Indiya da Nepal da kuma Najeriya, waɗanda ya zarga da ƙarancin dokokin kare wannan ruwa da ke ƙarƙashin ƙasa, da kuma rashin bin doka ko kuma tsare-tsaren da aka tanada domin kare wannan ruwa.
Binciken ya ce ruwan da ke karkashin ƙasa na iya jurewa fari na dogon lokaci, kuma yakan zama wata garkuwa a lokacin da ake fama da karancin ruwan sama.
Sai dai ana ganin mahukunta ba su fiye tsare-tsare da ruwan karkashin kasa ba, duk kuwa da muhimmancinsa.
Wannan ya janyo yadda ake amfani da shi fiye da ƙima, kuma a wasu lokutan a yi ta gurbata shi ba tare da tsawatarwa ba.

Asalin hoton, WaterAid
Dalilin binciken
WaterAid ta ce ta ƙaddamar da wannan bincike ne domin karewa da kuma tabbatar da wanzuwar ruwan ƙasa a cikin kasashen da take aiki kamar Najeriya da Indiya.
Duk da cewa ruwan karkashin kasa ya mamaye kusan kashi 30 cikin 100 na sararin duniya, wanda kuma ruwa ne da ke buɗe ba masu lura da shi.
Yana buƙatar masu lura da shi saboda matsalar sauyin yanayi ka da ta shafe shi, wadda za ta iya janyo karancinsa ta kuma shafi ingancinsa, saboda yadda yake iya jurewa lokacin fari kuma rana ba ta iya kona shi.
Da manufofi mai kyau za a iya cimma daya daga cikin muradan ƙarni, na tabbatar da samar da tsaftataccen ruwa ga kowa a fadin kudina.











