Yajin aikin ASUU: Daliban jami'o'i sun koma roƙon ASUU da gwamnati

Jami'ar Bayero

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Batun inda aka kwana kan yajin aikin ƙungiyar malaman jami'o'i ta ASUU na ci gaba da jan hankalin ɗalibai bayan shafe watanni bakwai suna zaune a gida.

Tun a watan Maris ƙungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki, kuma har yanzu babu ranar janye yajin aikin inda ƙungiyar kan kan bakarta.

An kammala taron ranar Laraba tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin ASUU ba tare da cimma matsaya ba.

Bayan kammala taron, ministan ƙwadago Chris Ngige, ya ce gwamnatin Tarayya ba za ta iya biyan Naira biliyan 110 na farfaɗo da jami'oin da ƙungiyar malaman ke ɓukata.

Wannan ya ja hankalin ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta na intanet kan yajin aikin da ya ƙi ci yaƙi cinyewa inda yawancinsi musamman ɗaliban ke rokon ɓangarorin biyu su sasanta a janye yajin aikin.

Ƴan Twitter da dama ne musamman suka bayyana takaci da kuma miƙa ƙoƙon bararsu ga wadannan bangarori biyu domin kawo karshen wannan yajin aiki, da ganin kowa ya koma bakin aikinsa daga Malaman har daliban.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

@ijere_uche ya yi kira ga ASUU ta janye yajin aikin saboda ya jefa ɗalibai cikin damuwa

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

@aystickz ya bayyana takaicinsa kan yajin aikin inda ya ce duk da takaddamar ASUU da gwamnatin Tarayya, mutum sai ya ƙara shekarar karatu

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Abdul Bapullo, ya ce rikicin ASUU da Gwamnatin tarayya, wannan rikici da ake ta kai rana a kai, ya janyo mana matsala ga tsarin karatunmu.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

line

Me ya janyo ce-ce-ku-cen a yanzu?

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar ta shiga wata tattaunawa da gwamnati wadda aka tashi ba tare da cimma wata manufa ba.

A yayin wannan tattaunawa ministan ilimi na kasar Adamu Adamu bai halarci taron ba, haka zalika shugaban hukumar jami'o'i ta kasar Abubuakar Rasheed bai halarci taron ba.

A karshen taron ministan kwadago Chris Ngige, ya ce gwamnati ba za ta iya biyan ASSU naira biliyan 110 ba, domin farfado da jami'o'i.

Ya kara da cewa matsalar tattalin arziki da kasar ta samu kanta ciki ta sanya gwamnati ba za ta iya biya ba, sai dai kuma gwamnatin ta yi wa ASSU ta yin biliyan 20 domin farfado da jami'o'in.

Zaman kashe wando

Ɗaliban jami'oin na Najeriya kusan kimanin wata bakwai ko takwas kenan suna zaman kashe wando sakamakon annan yajin aiki da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Amma yajin aikin ASUU ba wani sabon abu ba ne na kwashe watanni ko shekara ana yakin aiki.

Hakan na mayar da masu karatun shekara hudu su koma shekara biyar ko kuma masu shekara biyar su koma shida.

Idan mutum ya haɗa da bautar ƙasa da sauran tsare-tsare irin su bikin kammala jami'a zai kasance an doshi shekara bakwai a makaranta.

Wannan ya sanya 'yan jami'a a kasar fidda rai da wannan shekara a tsarin karatunsu, wadda ko da babu yajin aiki dama ta gamu da matsalar Covid-19.

line

Buƙatun ASUU

Farfesa Haruna Musa shi ne shugaban ASUU reshen jami'ar Bayero Kano, kuma a baya-bayan nan ya shaida wa BBC irin buƙatun da ƙungiyar ke son a biya mata kafin komawa bakin aiki.

Farfesan ya ce sun jima suna yarjejeniya da gwamnatin tarayya a kan bukatun da suke son a biya musu, amma har yanzu ta gaza aiwatar da su.

Ya ce,"Abubuwan da suke cikin yarjejeniyoyin da suka cimma da gwamnatin, abubuwa ne wadanda idan aka bi su ko shakka babu jami'o'in kasar za su dawo hayyacinsu".

Ga buƙatun na ASUU :-

  • Samar da wadatattun kudi wanda za a yi ayyuka domin farfado da jami'oi
  • Da biyan alawus na malamai wanda ya taru har ya kai shekara biyar zuwa shida ba a biya ba
  • Da matsalar yadda jihohi ke kirkirar jami'o'i barkatai ba tare da yi musu tanadi na wadatattun kudade ba domin tafiyar da su
  • Akwai batun samar da wani kwamiti da zai rika ziyartar jami'o'in gwamnatin tarayyar domin ganin irin ayyukan da suke yi don gano nasarori da ma matsaloli da aka samu
  • Da kuma batun sabon tsarin biyan albashi na bai daya da gwamnati ta ɓullo da shi na IPPIS wanda shi ma ya zamo matsala babbaru.