Akwai yiwuwar za a ƙara faɗawa yakin basasa a Afghanistan

Mai bada shawara kan harkokin tsaro a Afghanistan ya yi gargaɗin faɗawar ƙasar cikin wani sabon yaƙin basasa.

Hamdullah Mohib, ya shaida wa BBC cewa gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa don kaucewa shiga wannan barazanar.

Kalamansa ya zo ne bayan tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Afghanistan da ƴan Taliban ta tsaya cak.

Mr Mohib, ya bukaci mayakan Taliban da su tsaya a cimma yarjejeniya da manufa mai kyau, yayin da ake samun ƙaruwar tashin hankali da rikici wanda gwamnatin ta ɗora alhakin hakan kan ƴan Taliban.

To sai dai kuma ƙungiyar ta Taliban ɗin ta musanta wannna zargi.

Mr Mohib ya ce taimakon kai hare-hare ta saman da Amurka ke musu yanzu ya janyo musu cikas wajen samun nasarar kai wa ga ƴan Taliban din.

A wata mai zuwa ne ake sa ran dakarun ƙarshe na Amurka da ke Afghanistan za su bar Afghanistan bayan sun shafe kusan shekaru 20 a can.