'Yar shekara 15 da ta dauki bindigar AK47 don kare iyayenta

Wata matashiya 'yar Afghanistan ta samu yabo a kafafen sada zumunta bisa gwanintar da ta nuna bayan yaƙar wasu 'yan Taliban biyu da suka kashe iyayenta.

Yarinyar ta yi amfani da bindigar gidansu ƙirar AK-47 wajen harbe mutanen tare da raunata wasu da dama, a cewar jami'ai a Lardin Ghor.

Jami'an sun ƙara da cewa 'yan Taliban ɗin sun je gidan saboda mahaifin yarinyar yana goyon bayan gwamnati.

Wani hoton yarinyar riƙe da bindiga dai ya karaɗe shafukan sada zumunta a 'yan kwanakin nan.

Daga baya kuma ƙarin mayaƙa sun sake dirar mikiya a gida da ke ƙauyen Griwa amma kuma al'ummar yankin da mayaka masu samun goyon bayan gwamnati suka fatattake su.

Jami'ai sun ce tuni aka kai matashiyar da shekarunta ba su wuce tsakanin 14 da 16 ba da ƙaninta wani waje domin kare su.

Ma'abota shafukan sada zumunta dai sun jinjinawa matashiyar.

"Mun jinjina mata saboda bajintar da ta yi", kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito Najiba Rahmi na faɗa a shafin Facebook.

"Mun san ba zai yiwu a maye gurbin iyaye ba amma martanin da kika yi zai sa ki samu ɗan kwanciyar hankali," a cewar Mohamed Saleh shi ma a Facebook.

A cewar kafafen yaɗa labaran ƙasar, Ghor ɗaya ne daga cikin Lardunan yammacin Afghanistan da ya fi fama da rashin ci gaba sannan a lokuta da dama mata a yankin na fuskantar cin zarafi.

Ƙungiyar Taliban ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka a Fabrairu amma da dama daga mambobinta sun ci gaba da neman a hamɓarar da gwamnatin Afghanistan mai ci da kuma soke kundin tsarin mulkinta.