Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugaban Taliban ya tsere daga hannun jami'an tsaro
Wani kusa a kungiyar Taliban Ehsanullah Ehsan ya tsere daga inda jami'an tsaro ke tsare da shi a kasar Pakistan.
Hukumomin kasar sun tabbatar da hakan a ranar Lahadi kwana biyu bayan Ehsanullah, wanda ya shekara biyu a hannunsu ya yi ikirarin tserewa zuwa Turkiyya a wani sauti da ya fitar.
Wani babban jami'in tsaron Pakistan ya ce Ehsanullah shi ne tsohon kakakin kuniygar Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP), kuma yana da muhimmanci wajen samun bayanai a kan masu tayar da kayar baya.
Ana alakanta Ehsanullah da hare-haren da TTP ke kaiwa, ciki har da harin bam din da aka kai wa matashiya mai fafutakar ilimi Malala Yousafzai, a shekarar 2016. A 2017 ne ya mika kansa ga hukuma.
Wasu hirarrakin talbijin da aka yi da shi sun fusata 'yan kasar da suka zargi gwamnati da lallaba Ehsanullah bayan ya yi shekaru yana jagorantar masu zubar da jini.
Hukumomin tsaron kasar sun sha bayyana cewa mutumin ya ba su bayanan sirri da suka taimaka a yaki da suke yi da masu tayar da kayar baya.
Pakistan ta shafe gomman shekaru tana fama da masu ikirarin jihadi na cikin gida.
Hare-haren kungiyoyin sun hallaka dubban fararen hula da jami'an tsaro musamman bayan kafa kungiyar TTP a shekarar 2007.
A shekarar 2019 an samu raguwar hare-haren masu tsattsauran ra'ayi da raguwar kashe-kashen da suke yi fiye da koyaushe daga 2007 zuwa 2019.
Kwararru sun danganta nasarar da matakan sojin da kasar ta dauka a arewacin Waziristan da Khyber - cibiyar kungiyar Taliban - da kuma a birnin Karachi.
Karfin kungiyar TTP ya ragu sosai a 2018 bayan Amurka ta kashe shugaban kunigyar a Afghanistan, Maulana Fazlullah a wani harin sama.