Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Comet Neowise: Tauraruwa mai wutsiya ta fito fili cikin shekara 6,800
Masu hangen sama sun hangi wata hamshaƙiyar tauraruwa mai wutsiya yayin da take tunkarar wajen duniyar Earth.
An gano tauraruwa Comet Neowise ne a ƙarshen watan Maris sannan ta zama ɗaya daga cikin taurari masu wutsiya na ƙarni na 21 da ake iya gani da ido.
Tauraruwar za ta kasance kusa da duniya a ranar 23 ga watan Yuli, amma duk da haka nisanta da duniyar zai kasance kilomita miliyan 103.
Ga wuraren da suka riga suka gan ta, abin da mutane ba su saba gani ba a rayuwarsu.
An ɗauki wannan hoton ne da dare na sararin samaniyar Saltburn da ke Burtaniya.
Ana iya ganinta ne a samaniyar arewacin duniya - ƙasashen da ke Turai kenan da Amurka da Canada - jim kaɗan kafin faɗuwar rana da fitowarta.
Wasu mutanen da ke wajen Burtnaiya ma sun samu ganin ta.
An ɗauki wannan hoton na Neowise ne a saman wata coci a ƙasar Rasha.
Tauraruwar ba za ta sake wucewa ta kusa da duniya ba har sai nan da shekara 6,800, saboda haka wannan biki ne na rana guda ga duk wani mai rai a duniya a yanzu.
Wannan hoton tauraruwa mai wutsiya ne a saman duwatsun Rocca Calascio da ke Italiya.
A ranar 23 ga watan Yuli, tauraruwar za ta yi nisan ninki 400 na yadda wata ya yi wa duniya.
Sai dai duk da haka za ku iya ganinta ba tare da amfani da wata na'ura ba - ko da yake dai za su taimaka.
A nan, ana iya ganin tauraruwar a saman Van Province da ke ƙasar Turkiyya.
Tauraruwar comet wani dutse ne da ke zagaye da ƙwallon rana. Tana cike da duwatsu da kuma ƙanƙara, waɗanda su ma suke ɗauke da iskar gas.
Zafin da ke fitowa daga rana ne ke narkar da ƙanƙarar sannan ya saki iskar gas ɗin, wanda shi kuma yake haddasa doguwar jelar da muke iya gani daga duniyarmu.
An gano tauraruwar Neowise ne ta hanyar amfani da wata na'urar hukumar sufurin sararin samaniya ta NASA a ƙarshen watan Maris.
Lokaci na ƙarshe da ta zo kusa da rana ba ta samu wata matsala ba, yanzu kuma tana shirin komawa wajen zagayen ranar.
Mutane daga lungu da saƙo na duniya na ta ganin ikon Allah cikin annashuwa. Wannan hoton yana nuna tauraruwar ne a saman birnin Harbin da ke yankin Heilongjiang na China.
Za ta ci gaba da tafiya zuwa yamnmacin samaniya a tsawon watan Yuli.
Sannan daga tsakiyar watan za a riƙa ganinta a tsawon dare baki ɗaya amma 'yar ƙarama kuma a ɓangaren arewa.
Daga nan kuma ta ɓace a yuƙurinta na ficewa daga zagayen rana.
Kasancewar tauraruwa mai wutsiya ta fito fili, akwai yiwuwar a iya ganita a saman duniya.
An ɗauki wannan hoton ne a International Space Station.
Wani masanin taurari Ivan Vagner ya siffanta Tauraruwa Neowise a matsayin "wadda ta fi kowacce haske a cikin shekara bakwai da suka wuce. Ana iya ganin jelarta daga tashar sararin samaniya!"