Tsuntsu mai siffar jirgin yaƙi ya kafa tarihin yin tafiya mafi nisa a duniya

Tsuntsu fighter jet

Asalin hoton, Getty Images

Wani tsuntsu da masana kimiyya suka ce an halicce shi kamar jirgin yaƙi ya kafa sabon tarihi a matsayin tsuntsun da ya fi yin tafiya mai dogon zango a duniya.

Tsuntsun mai doguwar jela ya tashi daga Alaska da ke Amurka, inda ya sauka a New Zealand, bayan shafe kwanaki 11 yana tafiya ba tare da yada zango ba, abin da ke nufin cewa ya yi tafiyar a ƙalla kilomita 12,000.

Masana kimiyyar sun ce sun riƙa bin sawunsa ta hanyar wata na'urar bibiya ta zamani.

Sun ƙara da cewa tsuntsaye nau'ukan wanda ya nuna wannan bajinta a yanzu, ba sa bacci yayin da suke tafiya, hasalima sukan iya tsamurewa don rage girman jikinsu ta yadda za su yi doguwar tafiya ba tare da wata gajiya ba.

Dakta Jesse Conklin, na ƙungiyar Global Flyway Network ta masana kimiyya da ke bincike kan halittu masu ƙaura ya ce: ''Suna da wani irin ƙarfi na rashin gajiya.

''Akwai abubuwa da yawa a tattare da su. An halicce su tamkar tsarin jiragen yaƙi. Suna da dogayen fukafukai da ke taimaka musu yin abubuwa tamkar na jirgin sama.''

Tsuntsun wanda jinsin namiji ne da ake wa laƙabi da 4BBRW da ake alaƙantawa da launin shuɗi da ja da kuma fararen zobuna da aka maƙala masa a ƙafafunsa, an kuma maƙala masa wani ɗan ƙaramin tauraron ɗan adam mai nauyin giram biyar a ƙasan bayansa, don bai wa masana kimiyyar damar bibiyar halin da yake ciki.

Yana ɗaya daga cikin huɗun da za su bar cikin laka a Alaska, inda a can ne suke rayuwa suna tsintar tsutsa da tanar da suka kasance abincinsu tsawon wata biyu.

Dakta Conklin ya ƙara da cewa: ''Alamu sun nuna tsuntsayen sun san a inda suke a faɗin duniya. Ba za mu iya bayani sosai ba amma dai kamar suna da taswira.

''Suna shawagi ta saman tekun Pacific tsawon kwanaki a inda babu dandaryar ƙasa. Daga nan sai su shiga New Caledonia da Papua New Guinea inda ake da tsibirai kaɗan.''