Yadda tsuntsaye jam-baki ke yi wa manoma ta'adi a Sokoto

Sokoto

Manona a jihar Sakkwato a shiyyar arewa-maso-yammacin Najeriya na neman dauki daga hukumomin kasar wajen yaki da tsuntsaye masu jan-baki da suka afka wa gonaki a sassa daban-daban na jihar inda suke cinye amfani gona.

Wannan dai na zuwa yayin da ake fargaba game wadatar abinci a yankin a bana sakamakon yadda 'yan fashin daji suka hana yin noma a yankuna da yawa da ke shiyyar ta arewa a maso yamma.

Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza ya ziyarci wasu gonaki a kauyen Tudun-Mai-Tandu na karamar hukumar Dange Shuni domin gane wa idanunsa irin ta'adin da tsuntsayen ke yi wa shukar da suka yi.

Umaru Garba Shuni na daya daga cikin masu gonakin da tsuntsayen ke yi wa barna.

" Tsuntsaye ne baki da ake kira masu jan baki. Kuma sun shiga gonata inda suke cinye min geron da na shuka. Yanzu kusan ko'ina wannan tsuntsu na cinyewa jama'a amfani. Kuma ka san irin yanayin da ake cikia halin yanzu."

Shugaban kungiyar manoma ta AFAN a yankin na Karamar hukumar Dange Shuni Alhaji Sambo Abubakar, ya ce kutsen tsuntsaye ya tayar musu da hankali matuka abin da yasa suka yi sauri suka rubuta rahoto zuwa ga uwar kungiyar a matakin jiha domin neman dauki.

"Gaskiya zuwan wadannan tsuntsaye abin takaici ne domin duk gonar da ka duba zangarniya kawai kake gani. Ina samun korafe-korafe daga wurin mutane ba dare ba rana."

To sai dai Alhaji Sambo ya ce kafin daukin gwamnati ya zo, manoma a yankin na amfani da wani salo na gargajiya wajen korar tsuntsayen.

"Iyaye da yaransu kan kwashe yini a gonakinsu inda suke korar tsuntsayen ta hanyar buga kwanuka. To idan tsuntsayen suka ji karar kwanukan sai su tashi. Haka kuma ana amfani da zaren kaset na bidiyo inda ake kada zaren domin korar tsuntsaye.

Sai dai ga alama wannan ba zai yi wani tasirin a zo a gani ba; kuma dorewa da shi ba abu ne mai yiwuwa ba.

A cewar Murtala Gagadu Minannata shugaban kungiyar manoma a jihar, ko baya ga karamar hukumar ta Dange-Shuni, sun samu rahotannin mamayar tsuntsaye a yankunan kananan hukumomi daban-daban irin su Isa, da Sabon-birni, da Wurno, da kuma Wammako.

Wannan ne in ji shi ya sa kungiyar rubuta sakon neman agaji zuwa ga hukumomin aiki gona a jihar da kuma tarayya, sai dai har yanzu agajin bai zo ba.

Kwamishinan aikin gona na jihar Muhammad Arzika Tureta ya shaida min cewa sun samu koken manoman kuma tuni sun tura shi zuwa ga hukumomin tarayyar wadanda su ne ke da alhakin yaki da kutsen tsuntsayen wadanda suka shigo jihar daga makwabtan kasashe.

A watan Yuni, gwamnatin tarayyar kasar ta sanar da ware Naira biliyan 13 da miliyan dari tara wajen yaki da halittun da ke lalata shuka da kuma addabar dabbobi ciki har da tsuntsayen masu kaura daga wannan kasa zuwa wata a jihohi goma 12 na arewacin kasar da suka hada jihar ta Sakkwato. Sai dai manoma a jihar na cewa su gani a kasa.