EndSars: Tasirin da mawaƙa da ƴan fim ke da shi wajen kawo sauyi a Najeriya

- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau
- Lokacin karatu: Minti 4
Bayan dubban hotuna da bidiyo na wuraren shaƙatawa da na bukukuwa da aka saba gani a shafukan sada zumunta na taurari, a 'yan kwanakin nan ba haka abin yake ba.
Daga mako ɗaya zuwa yanzu, shafukan mawaƙa da taurarin fina-finai a faɗin Najeriya cike suke da yekuwar neman 'yanci da kawo ƙarshen cin zarafi ga 'yan ƙasar a kudu da arewacin ƙasar.
Muna iya tuna yadda Azeez Fashola - wanda aka fi sani da Naira Marley - ya yi barazanar shirya zanga-zangar neman rushe rundunar 'yan sanda ta SARS amma daga ƙarshe suka sasanta da 'yan sanda, inda kakakin rundunar Frank Mba ya tattauna da shi kai-tsaye ta Instagram.
Kazalika, mun ga yadda taurarin Kannywood da mawaƙan Hausa Hip Pop da 'yan ƙwallo suka riƙa amfani da maudu'in #EndNorthBanditry domin kira ga gwamnati da ta kawo ƙarshen kashe-kashen rayuka da 'yan fashi ke yi a Arewacin Najeriya.
Rahama Sadau da DJ Ab da Deezzel da Ali Jita da Ahmed Musa da Shehu Abdullahi na daga cikin waɗanda suka fi kowa ɗaga murya daga sashen arewaci.
Bugu da ƙari, mawaƙi David Adedeji Adeleke wato Davido ya ce zai yi wata ganawa ta musamman da Sufeto Janar Mohammed Adamu a Abuja ranar Litinin.
A bayyane yake cewa wannan fafutuka ce sanadiyyar rushe rundunar SARS, wadda aka sha yi wa zargin cin zarafin al'umma da azabtarwa.
Wannan ba sabon abu ba ne a wasu ƙasashe idan aka tuna fafutukar #MeToo, wadda taurari mata musamman a faɗin duniya suka riƙa bayyana irin cin zarafin da suka fuskanta a wuraren ayyukansu da kuma fafutikar #BlackLivesMatter.
#EndSars #EndSarsNow #EndPoliceBrutality #SarsMustGo
An tattauna a kan maudu'in #EndSars da makamantansa sau fiye da miliyan bakwai a dandalin Twitter cikin 'yan kwanaki.
Taurarin fina-finai da 'yan ƙwallon ƙafa da mawaƙa daga sassan duniya da dama sun goyi bayan fafutukar rushe rundunar SARS a cikin mako guda da ya gabata.
Mawaƙiya Tiwa Savage ta ce "rushe SARS bai wadatar ba akwai sauran matsaloli da ya kamata a gyara".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Mawaƙiya Dija ta ce "har yanzu akwai sauran aiki domin kawo ƙarshen azabtarwar 'yan sanda".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Ɗan wasan Arsenal Mesut Ozil ya ce "abin da ke faruwa a Najeriya abin tashin hankali ne, ya kamata mu yi ta kwarzanta maganar a ko ina da ina".
Ɗan wasan gaba na Chelsea Tammy Abraham ma ya yi kira da a kawo ƙarshen SARS.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Taurarin Kannywood da maudu'in #EndNorthBanditry
Yayin da ake tsaka da yekuwar kawo ƙarshen SARS a Najeriya, sai ga maudu'in neman kawo ƙarshen 'yan fashi a Arewa ya kunno kai a ranar Juma'a, 9 ga watan Oktoba.
Maudu'in #EndNorthBanditry na cikin waɗanda suka fi shahara a ranakun ƙarshen mako - wanda ke nufin a kawo ƙarshen fashi a Arewa.
Taurarin fim da mawaƙan Hausa Hip Pop ne kan gaba a wannan fafutikar.
Rahama Sadau ta wallafa saƙo ɗauke da maudu'in #EndNorthBanditry aƙalla sau bakwai a Twitter tun daga ranar Juma'a, har ma ta yi kiran da a gudanar da zanga-zanga.
"Wace irin ɗaga murya ake so mu yi kafin a saurare mu? A shirye muke," in ji Rahama Sadau.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Mawaƙin Hausa Hip Pop Haruna Abdullahi - wanda aka fi sani da DJ Ab - ya yi amfani da #EndNorthBanditry fiye da sau 10 baya ga yaɗa wasu saƙonnin masu ɗauke da maudu'in.
"['Yan sanda] Ku tura wata runduna ta daƙile fashi da garkuwa da mutane a Arewa. Titunammu ba lafiya suke ba," DJ Ab ya faɗa a ɗaya daga cikin saƙonnin.
Shi ma mawaƙin Kannywood Ali Jita ya tofa albarkacin bakinsa kusan sau 10. "Wane ne jagoran zanga-zanga, a shirye muke mu fito," in ji shi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 5
Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na tawagar Super Eagles ta Najeriya, Ahmed Musa ma ba a bar shi a baya ba, inda ya ce "ina fatan za a zage damtse wurin kawo ƙarshen wahalhalun".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 6
Shi kuma ɗan ƙwallon Najeriya Shehu Abdullahi - mai wasa a wata ƙungiya ta ƙasar Turkiyya - cewa ya yi: "Wannan kira ne na musamman ga gwamnonin Arewa, akwai buƙatar kawo ƙarshen fashi a Arewa."
Sai dai ba a ji ɗuriyar manyan taurari kamar su Ali Nuhu da Hadiza Gabon da Adam Zango da Fati Washa ba a fafutikar - amma Ali Nuhu da Washa sun yaɗa saƙonnin wasu da suka wallafa da maudu'in #EndNorthBanditry.
Kamar yadda DJ Ab yake tambaya: "Tun da dai yanzu an rushe SARS, ko za mu mayar da hankali kan daƙile 'yan fashi a Arewa?
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 7
Abin jira a gani shi ne ko fafutikar #EndNorthBanditry za ta yi tasirin da #EndSars ta yi.