Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Covid-19: An garzaya da Donald Trump asibiti bayan ya kamu da cutar
Kafar talabijin ta CNN ta yaɗa wani sautin hirar da ɗan jarida Bob Woodward ya yi da Donald Trump a watan Afrilu, inda shugaban ya bayyana cewa ba ya tsoron kamuwa da cutar korona.
Duk da cewa Trump ya yarda cewa cutar annoba ce "da ka iya kashe mutum", an sha ganinsa yana yawo ba tare da takunkumi ba tare da karya dokar nesa-nesa da juna.
"Akwai yiwuwar ka kamu da ita fa," Woodward ya tambaye shi yayin tattaunawar. "Yadda kake yawo a bainar jama'a kana cakuɗuwa da su, ba ka wata fargaba?"
"A'a, ba na fargaba. Ban san me ya sa ba. Ba fargaba," a cewar Trump.
"Me ya sa," Woodward ya sake tambaya.
"Ban san me ya sa ba. Kawai dai ni ba na wata fargaba."
Fadar White House ta sanar da cewa an an kai Donald Trump asibiti kasa da sa'a 24 bayan ya kamu da cutar korona.
Mista Trump ya fara nuna alamun kamuwa da cutar ta Covid-19 ne ranar Alhamis bayan da ya sanar da cewa shi da matarsa sun killace kansu cikin daren Laraba.
An fara ba shi wasu magunguna, kamar yadda likitocinsa suka ce "domin samar da matakin rigakafi" a matakin farko.. Jami'an Fadar White House sun ce shugaban yana fama da "alamun galabaita, amma yana cikin hayyacinsa."
An tafi da shugaban zuwa asibitin Walter Reed National Military Medical Centre ne.
Wani kakakin Fadar ta White House ya fitar da wata sanarwa: "Shugaba Trump na cikin hayyacinsa, amma ya fara nuna alamun kamuwa da cutar korona, sai dai ya yi ayyukansa duk tsawon yinin yau."
Sanarwar ta kuma ce shugaban na mika godiyarsa ga jam'an da suka damu da halin da shi da matarsa suke ciki.
Walter Reed asibiti ne da ke wajen birnin Washington DC, kuma shi ne asibiti mafi girma da shahara cikin dukkan asibitocin sojojin Amurka. A nan ake kai shugabannin Amurka idan za a duba lafiyarsu a kowace shekara.
Likitan shugaban Sean Conley ya yi wani jawabi da safiyar Juma'a, inda ya ke cewa "mun ba shugaban maganin gram 8 na Regeneron, wanda aka ba shi domin rage karfin kwayar a jikinsa.
An kuma ba shi magunguna kamr zinc, da vitamin D, da famotidine da kuma aspirin, inji Likita Conley.
"Da yammacin yau ya kasance cikin hayyacinsa amma ya galabaita kadan." Sanarwar ta kuma ce matar shugaban Melania ma na "fama da dan tari da da kuma ciwon kai."
Wannan labari ne da ka iya sauyawa domin a yanzu lamarin ke faruwa, kuma za mu rika wallafa sababbin bayanai da zarar sun bayyana. Sai a ci gaba da bibiyar wannan shafin domin sanin halin da ake ciki.