Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Aouar, Rice, Rudiger, Fati, Torreira, Kante

Lyon za ta bukaci a biya ta euro (£46m) kafin ta sayar da dan wasan Faransa Houssem Aouar, mai shekara 22, bayan ta ki karbar tayin Arsenal na euro 36m (£32.8m) kan dan wasan. (RMC Sport)

A shirye Arsenal take ta kara kudi zuwa £36.5m da kuma £9m na tsarabe-tsarabe domin dauko dan wasan na Lyon Aouar. (Football London)

Chelsea za ta mika fiye da £40m don karbo Declan Rice kuma ta yi amannar cewa kudin sun isa ta dauko dan wasan na Ingila mai shekara 21 saboda West Ham na bukatar masu gidan rana sosai. (Sun on Sunday)

Sai dai ita ma West Ham tana son karbo aron dan wasan Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 27, daga Chelsea. (Sun on Sunday)

Barcelona ta ki amsa tayin sayar da dan wasan Sufaniya mai shekara 17 Ansu Fati a kan euro 125m (£114m), da kuma karin euro 25m (£22.8m) na alawus-alawus. (Marca - in Spanish)

Real Madrid na son bayar da aron Luka Jovic sai dai tsohuwar kungiyarsa Eintracht Frankfurt ba ta son sake daukar dan wasan na Serbia, mai shekara 22. (AS - in Spanish)

Torino ba ya son dauko dan wasan Arsenal Lucas Torreira kuma duk da yake Atletico Madrid na ci gaba da sha'awar dauko shi, amma Arsenal ta fi so ta sayar da dan wasan na Uruguay, mai shekara 24, gaba daya kawai. (Football London)

Dan wasan Chelsea dan kasar Faransa N'Golo Kante, mai shekara 29, ya shiga kasuwa don haka a shirye yake ga mai son sayensa. (Sunday Express)

Dan wasan Liverpool mai shekara 20 Rhian Brewster yana so ya yi magana da Crystal Palace a kan yiwuwar tafiyarsa can a kan £20m move, kodayake Sheffield United da Aston Villa suna son dan wasan na Ingila mai buga gasar 'yan kasa da shekara 21.(Sun on Sunday)

Manchester City na shirin sabunta kwangilar dan wasanta na tsakiya Phil Foden, inda za ta kara albashin dan wasan mai shekara 20 daga £30,000 zuwa fiye da £150,000 a duk mako. (90 min)