Botswana: Kun san cutar da ke yi wa giwaye kisan gilla?

Asalin hoton, Supplied
Wata guba cikin ruwa ce ta janyo mutuwar ɗaruruwan giwaye da a baya aka rasa abin da yake kashe su a Botswana, in ji jami'an da ke kula da gandun daji.
Botsawana gida ne ga kashi ɗaya bisa uku na giwayen Afirka da ake samun bayanan raguwarsu.
An fara magana kan batun lokacin da aka ga gawar giwaye a yankin Okavango tsakanin Mayu da Yuni.
Jami'ai sun ce kimanin giwa 330 aka tabbatar sun mutu sakamakon gubar cyanobacterial. An kuma soke batun da ke cewa akwai yiwuwar kashe giwayen ta hanyar da ba ta kamata ba ne yake haddasa mutuwarsu.
Ana samun ƙwayoyin cutar masu guba cikin ruwa wani lokacin suna girma ne.
Gargaɗi: Wasu ba za su ji daɗin ganin hotunan ba
Binciken ya biyo bayan watannin da aka shafe ana gwaji a ɗakunan gwaji da ke Afirka Ta Kudu da Canada da Zimbabwe da kuma Amurka.
Da yawan matattun giwayen an same su ne kusa da ramuka masu ruwa a ciki amma har zuwa yanzu, hukumomin kula da gandun daji sun bayyana kokonto cewa ƙwayar cutar ce ta haddasa mutuwar giwayen saboda furannin sun bayyana a gefen kududdufi sannan giwaye na son shan ruwa ta tsakiya.

Asalin hoton, Supplied
"Gwaje-gwajen da muka yi a baya-bayan nan sun gano ƙwayar cutar cyanobacterial neurotoxins ce abin da ya janyo mace-macen giwayen.
''Waɗannan ne ƙwayoyin cutar da ake samu a ruwa," kamar yadda Mmadi Reuben, wani babban likitan dabobbi a cibiyar kula da dabbobi ta ƙasar ya shaida wa wani taron 'yan jarida ranar Litinin.
A kusan ƙarshen watan Yunin 2020 ne aka daina samun mace-macen giwayen lamarin da ya yi dai-dai da lokacin da ruwa ke ƙafewa," kamar yadda AFP ta rawaito ya faɗa.
Rahotanni a watan Yuni sun ce ba a cire hauren giwayen ba.
Cyril Taolo, mataimakin darakta a cibiyar kula da namun daji, ya ce akwai tambayoyi da dama da har yanzu ba a amsa su ba.
"Akwai tambayoyi da muke buƙatar amsarsu kamar me ya sa kawai giwaye ne suke mutuwa kuma me ya sa a wannan yanki ne kaɗai. Muna da maganganu da yawa da muke bincike akai," in ji Cyril Taolo.

Asalin hoton, Supplied
Ɗaruruwan giwayen aka gani bayan da aka yi wani bincike ta sama a farkon shekarar nan.
Dr Niall McCann na kungiyar agaji ta National Park Rescue da ke Burtaniya, a baya ya shaida wa BBC cewa masu kula da muhalli sun fara sanar da gwamnati a farkon watan Mayu, bayan da suka yi wani kewaye a kan yankin.
"Sun hangi giwa 169 a cikin kewayen jirgin na sa'o'i uku," in ji shi. "Akwai abin mamaki kan yadda aka samu damar gani da ƙidaya giwayen a cikin sa'a uku.

Mece ce ƙwayar cutar cyanobacteria?

Asalin hoton, De Agostini/Getty Images
- Ana samun Cyanobacteria, a duniya musamman a cikin ruwa
- Wasu nau'ukan cutar suna sa guba da ke shafar dabbobi da mutane
- Mutane na iya kamuwa da cutar cyanobacterial idan suka sha gurɓataccen ruwan ko wanka a cikinsa
- Alamu sun haɗa da ƙaiƙayin jiki da kartar ciki da amai da tashin zuciya da gudawa da masassara da ƙaiƙayin maƙwagoro da ciwon kai
- Gubar da ke jawo cyanobacteria na iya shafar dabbobi da tsuntsaye da kifi.
Majiya: WHO












