Yarjejeniyar Isra'ila: Bahrain da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na tsaka mai wuya

Shugaban Amurka Donald Trump ya yaba wa abin da ya kira "sabuwar Gabas ta Tsakiya" yayin bikin kulla yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Haɗaɗɗiyar daular Larabawa da Bahrain.

Mista Trump na magana ne yayin da ƙasashen Larabawan na yankin tekun Gulf suka rattaba yarjeniyoyin mayar da cikkkiyar dangantaka da isra'ila.

Duka ƙasashen uku sun yaba wa yarjeniyoyin, suna cewa an kafa tarihi, kuma Mista Trump ma ya yi furuci irin wannan.

Ƙasashen Larabawan biyu sun kasance na uku da na huɗu cikin jerin ƙasashen da suka mayar da dangantakar da suka kwance da Isra'ila tun bayan da aka kafa ta a 1948.

Mista Trump na fatan sauran ƙasashen Larabawa za su bi sahun waɗannan ƙasashen biyu, amma Falasdinawa sun buƙaci sauran ƙasashen su juya wa matakin baya har sai an warware rikicin mamaye kasar Falasɗinuda Isra'ila ta daɗe tana yi.

Mista Trump ya ce "Bayan gomman shekaru na rarrabuwa da rikice-rikice, a yau mun kafa harsashin sabuwar Gabas ta tsakiya. Ya yi jawabi ne ga jama'ar da suka taru a Fadar White House a ranar Talata.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi maraba da yarjeniyoyin, yana cewa, "Wannan rana ce ta kafa tarihi; kuma tana albishirin samar da sabuwar hanyar zaman lafiya."

Amma shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya ce hanyar zaman lafiya ɗaya ce, wato Isra'ila ta janye daga yankunan Falasdinu da ta mamaye.

"Zaman lafiya, da tsaro da kuma ci gaban yankin za su samu ne kawai bayan da Isra'ila ta daina mamayar kasashen Falasdinu. Ya bayyana matsayarsa ne a wata sanarwa da ya fitar bayan da ƙasashen suka ƙulla yarjeniyoyin.

Sojojin Isra'ila sun ce an harba rokoki biyu daga cikin zirin Gaza zuwa cikin Isra'ila yayin da ake bikin kulla zaman lafiyar a Amurka.

Hankali zai koma kan sauran ƙasashen Larabawan da ke yankin, domin a ga ko su ma za su miƙa wuya ga bukatun Amurka. Kawo yanzu dai Saudiyya ta ce ba ta shirya ba tukuna.

Ana ganin yarjeniyoyin wata hanya ce da Amurka da kuma Isra'ila ke bi ta yaƙar Iran.