Yadda aka yi tiyata kan kunkuru mai shekara 80 da mota ta taka a Argungu

Likitocin dabbobi a Sokoto da ke arewacin Najeriya sun ceto wani kunkuru mai kusan shekara 80 da mota ta taka a farkon makon nan.

Likitocin da suka kai shida gami da jami'an jinya sun mayar wa da kunkurun kwanson bayansa da ya fashe sakamakon taka shi da mota ta yi a jihar Kebbi.

Jagoran likitocin Dr. Nura Abubakar ya shaida wa BBC cewa, motar ta taka kunkurun ne a Birnin Argungu na jihar Kebbi, har bayansa ya fashe.

Ya ce da farko sun bai wa kunkurun taimakon gaggawa ranar Litinin da daddare, sannan aka yi masa tiyata da safiyar Talata.

"Abin da muka yi masa shi ne mun hada wajen da zai iya haduwa da danyen bawon bayan nasa, sannan akwai inda ya tararratse da yawa da ba zai gyaru ba, sai muka samu wani abu muka rufe wajen, in ji Dr. Nura.

Ya kara da cewa tsawon wajen da ya fashe ya kai inci 12, fadinsa kuma ya kai inci bakwai.

Kwanson kunkurun yana ba shi kariya yana kuma yi masa amfani daidai da wajen da kunkurun ke rayuwa.

A cewar Dr. Nura kwanson kunkurun yana taimaka masa wajen sarrafa yanayin zafi da kuma taimaka masa yin iyo a ruwa.

Ya ce yana kuma taimaka masa wajen ba shi kariya daga abin da zai iya fado masa, da kuma manyan dabbobi da suke farautar kanana.

Likitan ya ce a yanzu kunkurun, wanda zai cika shekara 80 a watan Fabrairun badi, yana cikin koshin lafiya kuma za a sake yi masa wani aiki nan gaba.