Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dakatar da Farfesar da ta yi ƙaryar ita baƙar fata ce
Malamar jami'ar nan ta Amurka wadda ta ce ta yi ƙaryar cewa ita baƙar fata ce, ba za ta koyar da karatu a zangon karatu mai zuwa ba, kamar yadda Jami'ar George Washington ta Amurka ta tabbatar.
Jessica Krug, wadda Farfesa ce da ta mayar da hankali kan nahiyar Afrika da kuma'yan Afrikan da ke zama a ƙasashen waje, ta fito fili ta amince cewa ita asalin Bayahudiya ce daga birnin Kansas na Amurka.
Ta bayyana hakan ne a wani shafin intanet inda ta ce "Na gina rayuwata kan ƙin jinin baƙar fata."
Abokan aikinta sun bayyana cewa sun yi mamaki kan wannnan batun da ta bayyana wanda ba su yi tsammani daga wurinta ba.
A wani saƙo da Ms Krug ta wallafa, ta bayyana cewa ta yi ƙarya yayin da ta fake da cewa ita baƙar fata ce kuma asalinta ba haka ba ne.
A wata sanarwa da jami'ar George Washington ta fitar, ta bayyana cewa Ms Krug ba za ta koyar da ɗalibai ba kuma jami'ar ta ce malaman makaranta da ɗalibai da dama sun ji haushin abin da ta yi.
Babu tabbacin ko za ta ci gaba da aiki a jami'ar ko kuma za a sallame ta.
Wane martani aka mayar dangane da lamarin?
Abokan aikin Ms Krug a Jami'ar da ta ke koyarwa a tsangayar koyar da tarihi sun fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa inda suke kira da ta yi murabus daga muƙaminta ko kuma jami'ar su tasa ƙeyarta.
"Ta ci amanar ɗaliban makarantar da dama na yanzu da wadanda suka kammala karatu, da kuma ɗalibai masu karatu kan Afrika, da ɗaliban tarihi," in ji sanarwar.
"Sashen koyar da tarihi na mayar da hankali ne wurin fadin gaskiya kan lamuran da suka faru a baya. Irin abin da ta aikata, wannan zai sa a saka alamar tambaya kan duk wani bincike da Dakta Krug ta yi."
Wani ɗalibi da zai fara halartar ajin Ms Krug domin koyon tarihi kan yankin Latin Amurka ya shaida wa jaridar Washington Post cewa "ya samu karayar zuciya sakamakon ɗalibai sun zo su koyi tarihi daga wurinta kuma sun saka duk wata yarda a kanta."
Wasu daga cikin binciken da Ms Krug ta gudanar sun yi fice musamman kan tarihi da siyasar Afrika.