Prince Malik Ado Ibrahim, Adama Indimi: Me ya sa ‘yan Najeriya suka damu da bikin ‘ya’yan Indimi?

Lokacin karatu: Minti 3

Bikin 'yar gidan mashahurin attajirin nan Muhammadu Indimi Adama Indimi da angonta Prince Malik Ado Ibrahim ya zamo abin kwatance da kuma magana a shafukan sada zumuntan 'yan Najeriya.

An yi auren ne a rana Asabar 8 ga watan Augustan 2020.

Bayanan da BBC ta tattaro a kafafen yada labarai na kasar sun nuna cewa Adama ta auri babban dan Sarki Dr Ado Ibrahim di Ohinoyi a jihar Kogin Najeriya.

An ware wani shafe a Instagram wanda aka saka hotuna da bidiyon yadda aka gudanar da bikin.

An fara bikin ne da kunshi wanda aka yi a ranar Juma'a 7 ga watan Augustan 2020 a Maiduguri, inda aka daura aure a washegarin ranar wato Asabar.

Me ya sa 'yan Najeriya ke damuwa da bikin 'ya'yan Indimi da sauran masu kudi?

BBC ta tattauna da Aisha Falke, wadda take yawan wallafa abubuwan da suka shafi bukukuwa a shafin Instagram domin jin dalilin da ya sa mutane ke damuwa da bikin 'ya'yan masu hannu da shuni kamar Indimi.

Aisha Falke, ta ce "Ba wani abu ne ke sa mutane ke damuwa ko kuma son ganin hotuna da bidiyo na irin wadannan bukukuwa ba illa sha'awa, kuma bukukuwan irin wadannan mutane na armashi sosai saboda irin kudin da ake kashewa wajen shirya bikin".

Ta ce "Baya ga haka kuma, su 'ya'yan Indimi na da yawan gaske, sannan kuma ma'abota shafukan sada zumunta ne, ma'ana suna yawan wallafa hotunansu da ma bidiyonsu a shafukan sada zumunta".

Aisha Falke ta ce"Wani abu da ya sa mutane ke bibiyar bukukuwan irin wadannan mutane shi ne su 'yan gayu ne ga su kuma kyawawa, don haka mutane na son ganin irin yadda aka kece raini wajen kwalliya a irin wadannan bukuwa, shi yasa aka damu da bikin nasu".

Aisha ta ce, ga mata kuma suna son kallon hotuna da bidiyon irin wadannan bukuwa ne domin su ga dinkuna ta yadda zasu kai wa telolinsu su dinka musu irinsa suma.

Wace ce amarya Adama Indimi?

Adama Indimi, wadda mutane suka fi sani da Presido tana ayyukan jin sannan kuma tana da shagunan kayan shafe-shafe.

Kazalika an taba nada ta a matsayin darakta a lokacin zaben Shugaba Buhari na shekarar 2019.

A cewar wasu rahotanni ta taba soyayya da fitaccen mawakin nan dan Najeriya Dbanj.

Mahaifinta, Muhammadu Indimi, mashahurin dan kasuwa ne kuma shi ne shugaban kamfanin makamashi na Oriental, haka kuma siriki ne a wajen shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja Ibrahim Babangida.

Haka Indimi ma siriki ne ma a wajen tsohon ministan Najeriya Bashir Dalhatu.

Wanene Prince Malik Ado Ibrahim?

Yarima Malik Ado Ibrahim, dan sarki Ohinoyi ne na masarautar Ebira.

An haife shi a Najeriya amma ya yi karatu a Burtaniya da Amurka.

Angon shi ne ma mallakin kuma shugaban Nigus Enfinity da ke aiki tare da kamfanin BYD na China.

Ya yi fice wajen kere-kere a F1.

Yariman masoyin motoci ne kuma tun a 1990 ya ke harkar kera motoci.

Ya yi aiki da kamfanin Proton da Lotus sannan ya taimaka musu wajen inganta ayyukan Lotus da gwamnatin Malaysia ta bukata a 1999.

Shi ne bakar-fata na farko da ya yi aiki a Formula 1, ya na kuma sha'awarar tseren mota sosai.

Kalli wasu bidiyo na bikin