ICRC: Fiye da mutum dubu 40 sun bace saboda rikici a Afrika yawanci a Najeriya

Wasu ma'aikatan kungiyar agaji ta Red Cross a Najeriya

Asalin hoton, @ICRC

Bayanan hoto, Wasu ma'aikatan kungiyar agaji ta Red Cross a Najeriya

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross - ICRC ta ce fiye da mutum dubu 40 ne suka bace a Afirka sakamakon rikice-rikice da kaura da kuma sauyin yanayi.

Cikin wani rahoto da ta fitar kungiyar ta ce mafi yawancin wadanda suka bata mata ne da kananan yara.

Kungiyar ta ICRC ta ce al'amarin ya fi shafar Najeriya wadda take da mutum 23,000 da suka bace.

Aliyu Dawobe shi ne mai magana da yawun kungiyar a Najeriya ya kuma shaida wa BBC cewa, tun daga shekarar 2012 da kungiyar ta su ta fara aiki a Najeriya suke samun koken batan mutane da dama.

Daga cikin wadanda suka batan yara ne suka fi yawa inda suke da kaso 60 cikin 100 na dadin wadanda suka bata a Najeriya'' in ji shi.

Ya kara da cewa kaso 14 cikin 100 na wadanda suka batan yara ne.

Rikicin Boko Haram arewa maso gabashin Najeriya ya dai-daita garuruwa da dama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rikicin Boko Haram arewa maso gabashin Najeriya ya dai-daita garuruwa da dama

Aliyu Dawobe ya ce wadannan mutane da suka batan sun kasance ko ana nemansu ne ko kuma suna neman iyalansu.

Jami'in na ICRC, ya ce ''wadannan mutane ba wai suna wajensu ne a killace ba. a'a nemansu ake yi saboda 'yan uwansu ne suka kai kokensu wajensu daya ke sun san suna aiki irin wannan na sada 'yan uwa da 'uwa ko kuma iyaye da 'ya'yansu''.

"Mune da jami'an Red Cross na Najeriya muke hada gwiwa muke irin wannan aiki na neman wadanda muka samu koken sun bata, kuma iyalansu kan bamu hotunansu don mu samu sauki neman su".

Ya ce, "Muna zuwa sansanonin 'yan gudun hijra mu nemi irin wadannan mutane, haka idan yara muka samu suna neman iyayensu, mu kan tambayesu adireshi ko kuma sunan garinsu, sai mu fara neman iyayen nasu".

Jami'in ya ce, a shekarar da ta gabata ta 2019, sun sada iyalai da 'yan uwansu ko 'ya'yansu da suka kai fiye da 53.