Coronavirus a Madagascar: Maganin gargajiyar shugaban ƙasar ya gaza daƙile Covid-19

President Andry Rajoelina attends a ceremony to launch Covid Organics in Antananarivo - 20 April 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaban na tallata wani maganin cutar korona
    • Marubuci, Daga Raïssa Ioussouf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Antananarivo

Asibitoci a Madagasar na kokawar gano kan wani tashin gwauron zabi na masu kamuwa da cutar korona a kasar yayin da shugaban ke ci gaba da tallata sahihancin wani magani da ya ce yana warkar da cutar duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya ba ta amince da shi ba.

Masu fama da cutar sun nunka har sau hudu a ƙasar da ke yankin tekun Indiya inda akwai fiye da mutum 13,000 da suka kamu, mutum 162 kuma sun mutu.

Amma duk da tabarbarewar lamarin, Shugaban ƙasar Andry Rajoelina ya kafe cewa maganin gargajiyar mai suna Covid-Organics na da sahihanci. A watan Afrilu ya ƙaddamar da shi.

Hukumar Binciken Kimiyya ta Malagasy ce ke hada maganin daga wani tsiro mai suna artemisia - wanda kuma ake amfani da shi wajen magance zazzabin cizon sauro - da kuma wasu itatuwan na Malagasy.

An rika tallata maganin, ana cewa zai iya magancewa da aikin riga-kafin kamuwa da cutar - kuma a watanni hudun da suka gabata ana ba yara ƴan makaranta.

Malagasy schoolchildren at their desks with Covid-Organics bottles next to them - April 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A watannin da suka gabata ana ba yara ƴan makaranta maganin duk da babu tabbacin yana warkarwa

A farkon watan nan shugaban ya fita cikin gari yana raba wa al'ummarsa maganin tare da kayan masarufi kamar shinkafa da man girki da siga ga marasa galihun cikinsu a Antananarivo babban birnin ƙasar.

Ya sha sukar yadda yake tara mutane a wuri guda duk da cewa ana iya yada cutar ta wannan hanyar, amma ya kare kansa yana cewa "annobar za ta wuce kuma za mu kawar da ita".

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce tana maraa da yunkuri irin na Madagascar, amma tana son a tabbatar da akwai hujja ta kimiyya kafin ta amince da duk wani magani irin wannan.

Kawo yanzu babu wata hujjar da aka fitar da ke nuna cewa maganin na aiki - amma mutanen Afirka da dama na nuna shi a matsayin wani abin alfahari da nahiyar ta samar.

An aika da maganin kyauta zuwa wasu kasashen Afirka da dama.

2px presentational grey line

Gwamnatin ƙasar na kare kanta daga sukar da ta ke sha daga cikin gida da kuma ƙasashen waje.

"Duk da cewa muna da kororon roba, bai zama hujjar yin sakaci da cutar HIV/AIDS ba. HIV ta wuce ne? Yanayin iri daya ne", in ji kakakin shugaban ƙasar Rinah Rakotomanga.

A soldier distributes masks and samples of the Covid-Organics in Antananarivo - April 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sojoji sun raba wa mutane takunkumi da wasu kwalabe na maganin koronan a watan Afrilu

Amma ma'aikatar Lafiya ta kasar na takatsantsan da tallata maganin - inda ta ke ba asibitoci shawarar ba marsa lafiya maganin na Covid-Organics kwai idan cutar ba ta ci ƙarfin jikinsu ba, da kuma wadanda ba su da cututtuka kamar ciwon suga.

Ana kuma bukatar wadanda ke fama da cutar su amince kafin a fara ba su maganin.

Hospital ward in Antananarivo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Asibitocin birnin Antananarivo na fama da ƙaruwar masu cutar korona

Ma'aikatan jinya ba su da kayan kariya

Ma'aikatan jinya da ke kan gaba da kula da masu cutar korona na tsaka mai wuya, ciki har da wadanda ke babban asibitin ƙasar.

Emergency entrance to Joseph Ravoahangy Andrianavalona Hospital in Antananarivo, Madagascar
AFP
I treated him [a Covid-19 patient] without proper protective gear. I only had a cloth mask that I brought from home"
Sitraka Randrianasolo
Medic at Joseph Ravoahangy Andrianavalona Hospital
1px transparent line

Sitraka Randrianasolo mai shekara 27 likita ne a asibitin Joseph Ravoahangy Andrianavalona da ke babban birnin ƙasar. Ya ce akwai ma'aikatan jinya da yawa da suka kamu da cutar Covid-19 a ƴan makonnin nan.

"Akwai wani maras lafiya da aka zo da shi cikin gaggawa kuma ya mutu bayan sa'a 24. Ashe yana da korona."

Ya kara da cewa, "Na duba shi ba tare da kayan kariya ba. Wani takunkumi na yadi da nazao da shi daga gida kawai nake sanye da shi. Daga baya an gwada ni, kuma na gode wa Allah da ban kamu ba."

Duk da ana fargaba an dage dokar kulle

Gomman ma'aikatan jinya sun kamu da cutar ta korona.

Soldiers in a pick-up truck with the sign saying "Lutte Contre Covid-19" (Fight against Covid-19) in Antananarivo, Madagascar - April 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaban ƙasar ya ce akwai wani sirin samar da mafita da gwamnatinsa ke aiwatarwa a babban birnin ƙasar

Fargabar kamuwa da cutar ba su ragu ba duk da dage dokar kulle wanda aka yi na mako biyar kawai da gwamnatin ta yi a yankin Analamanga - wanda shi ne yankin da babban birnin kasar yake.

Shugaba Rajoelina ya bayyana a wani jawabin talabijin cewa ba zai yiwu mutanen kasar su ci gaba da rayuwa a cikin kulle ba. Ya ce yanayin zai iya karya tattalin arzikin kasar.

Amma yankin na Analamanga ya kasance wanda lamarin yafi ƙamari - kuma annobar na ƙara bazuwa a sauran yankunan da ke tsibirin.