Maganin gargajiya na Madagascar: Buhari ya amince a karɓo maganin coronavirus

Buhari

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin karɓo kason Najeriya na ganyen shayin Madagascar da shugaban kasar ya ce yana maganin cutar korona.

Sakataren gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, shugaban kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da korona ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake yi wa manema labarai bayani, kamar yadda aka saba kan cutar korona a Najeriya da kuma matakan da gwamnati ke ɗauka.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Ya ce shugaba Buhari duk da ya amince a karbo maganin na Madagascar, ko da yake ya kara da cewa dole sai ya bi tsari na tabbatar da ingancin magunguna.

Karin bayani kan coronavirus

Madagascar tuni ta aika wa kasashe da dama na Afirka da maganin kyauta, kuma ta tura zuwa Guinea Bissau.

Najeriya ta ce ya kamata ta karɓo nata kason daga Guinea Bissau.

Ya zuwa daren Lahadi, mutum 4399 aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Najeriya, mutum 778 suka warke yayin da mutum 143 suka mutu.