Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Irin shaƙuwar da ke tsakanin 'yan kasar Afirka ta kudu da barasa
Haramta shan barasa lokacin ɓarkewar annobar korona ya ja ra'ayin wakilin BBC Vunami Mkhize yin waiwaye kan dalilin shaƙuwarsa da ƙasarsa da barasa.
Ina ɗan shekara 17 a shekarun farko na makaranta na fara ɗanɗana barasa da kuma shiga hali na maye wanda har ya kai ga kora ta daga makaranta a 2002.
Na dawo daga makarantar Ixopo da ke yankin Kwazulu Natal wanda ke kewaye da tsaunuka waɗanda marubucin da ke ƙyamar wariyar launin fata Alan Paton ya bayyana a matsayin ƙasar da aka fi ƙauna.
Paton malami ne a makarantar a 1920 kuma an rataye shafin farko na littafinsa a bangon ɗakin karatun makarantar. Ya sa ina son na yi koyi da shi - Na samu shafuka daga littafin da zan rubuta a daƙin karatu. Amma hakan ya kasance kafin hankali na ya ɗauku.
Lokacin da na fita daga tasi bayan hutun makaranta, ni da babban aboki na kai tsaye muka nufi wurin shan barasa da ke kusa inda muka sayi giya da kuma rabin kwalbar Vodka.
Wanda ke sayar da barasa bai nuna halin ko in kula ba game da sayar da giya ga matasa biyu, wanda ke bayyana sakaci a wasu masana'antu musamman idan an zo batun kula da buƙatun ƙananan yara.
Mun sha a wani kangon gida - kuma nan take na ji daɗin yanayin da na shiga duk kuwa da ɗanɗanon bai ratsa ni ba.
Daga lokacin da muka doshi tsauni zuwa makarantar kwana, dare ya yi kuma an rufe kofar shiga. Aka kira shugaban makaranta; aka tabbatar da makomarmu.
Na so a ce wannan ya kasance hali na ƙarshe da ya faru, amma na ci gaba da shiga irin wannan yanayin.
Amma ban taɓa yin nadama ba - na rubuta cewa irin wannan wata alamar ɓata ce mai daraja, wanda ya ja hankalin abokai yayin da kuma nake alfahari kan yawan lokacin da na kwankwaɗi barasa a ƙarshen mako.
Zamanin wariyar launin fata da aka haramta shan barasa
A Afirka ta kudu, halin da na shiga ba sabon abu ba ne, na tabbata mutane da dama suna dauke da labarai na al'ajabi da za su bayar.
Idan aka zo batun al'adar shan barasa a Afirka ta kudu shi ne yayin da mafi yawancin manya sun ƙaurace, waɗanda suke shan giya, suna sha sosai.
Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana mafi yawancin masu shan barasa a ƙasar a matsayin mashaya.
Hakan na nufin kusan kashi 59 na masu shan barasa suna shan sama da giram 60 na barasa akalla sau ɗaya a wata - cewa shan giya sau shida, fiye da sau huɗu a rana da aka shawarci maza.
Jami'in hukumar da ke gudanar da bincike kan magunguna a Afirka ta Kudu Charles Parry, wanda ya kwashe shekara fiye da ashirin yana nazari kan alakar kasar da barasa, ya yi amannar cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin dabi'armu ta shan barasa da kuma tahirinmu.
Farfesa Parry ya shaida min cewa gabanin kawo karshen mulkin tsirarun fata a shekarar 1994 cewa :"Akwai lokacin da ba a sayarwa bakar fatar Afirka ta kudu barasa."
Hakan ne ya sa masu shan giya suke zuwa mashayar da aka haramta, inda bakaken fata da dama suke kallon hakan a matsayin wata hanyar bijirewa mulkin farar fata.
A lardin Cape Winelands, galibi ana biyan leburori ladansu na aiki da barasa. Ko da yake an dade da daina wannan al'ada, amma ta riga ta yi tasiri a tsakanin al'ummomin da ke Western Cape.
Dabi'armu ta yawan kwankwadar barasa ce ta sanya gwamnati ta haramta shan giya a baki dayan kasar tun farkon lokacin da annobar korona ta barke a watan Maris, matakin da 'yan kasar suka yi fushi da shi.
Ranar 1 ga watan Yuni, an sake amincewa a rika sayar da barasa ga mutanen da za su sha a gidajensu, amma wata guda bayan haka an sake haramta sayar da ita.
A halin da ake ciki Afirka ta Kudu tana mataki na biyar cikin kasashen da suka fi fama da Covid-19, inda aka tabbatar mutum fiye da 500,000 sun kamu da cutar.
Tabarbarewar tattalin arziki
Haramta shan barasar ya taimaka wajen inganta kiwon lafiyar al'umma, sai dai ya kawo tabarbarewar tattalin arziki.
Masana'atun da ke yin barasa suna bai wa miliyoyin mutane aikin yi, kuma su ne suke samar da kashi 3 na tattalin arzikin kasar. Babbar masana'antar yin giya a nahiyar Afirka, South African Breweries (SAB), ta ce za ta fasa zuba jarin $285m a kasar saboda hanin da aka yi wa mutane na shan barasa.
"Soke zuba wannan jari shi ne ya sa aka yi asarar mako 12 na harkokin kasuwanci, wanda za a iya kwatantawa da da rasa kashi 30 na kayan da SAB ke sarrafawa," in ji Andrew Murray, mataimakin shugaban fannin kudi na kamfanin.
Heineken, kamfanin barasa na biyu mafi girma a Afirka ta Kudu, ya sanar da dakatar da shirinsa na zuba jari 6bn-rand wajen gina sabon kamfani a birnin Durban - da kuma kirkiro sabbin guraben aiki 400 a masana'antun da suka rasa fiye da ma'aikata 100,000 tun karshen watan Maris.
Ana kiraye-kiraye kan bari a sayar da barasa
Lucky Ntimane da ke kungiyar kwadago ta ma'aikatan kamfanonin barasa da ke Afirka ta kudu na cikin mutanen da ke kiraye-kiraye kan a bari a ci gaba da sayar da giya.
Ya ce says mutum fiye da 150,000 sun dogara da sayar da barasa wajen samar da abin da za su ciyar da iyalansu yana mai cewa matakin gwamnati na ko-oho a kan batun ya nuna "rashin kulawa da masana'ata mai albarka" irin wannan.