Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Masu cutar sun zarce rabin miliyan a Afirka ta Kudu
Mutane fiye da rabin miliyan ne aka tabbatar sun kamu da ƙwayar cutar korona a Afirka ta Kudu, cewar ministar lafiyar ƙasar.
Zwelini Mkhize ta sanar da gano sabbin waɗanda cutar ta harba har sama da mutum dubu goma ranar Asabar, abin da ya sa adadin ya kai 503,290, daga ciki kuma 8,153 sun riga mu gidan gaskiya.
Afirka ta Kudu, ɗaya daga cikin ƙasashe mafi bunƙasar tattalin arziƙi a Afirka, yanzu fiye da rabin mutanen da ke fama da cutar korona a ɗaukacin nahiyar suna ƙasar.
Lamarin dai ya sanya ta zama ƙasa ta biyar a jerin waɗanda suka fi fama da annobar kobid-19 a duniya, bayan Amurka da Brazil da Rasha da Indiya
Masu koronan dai yanzu haka sun fi dandazo ne a zagayen Pretoria babban birnin ƙasar, inda asibitoci ke fama da kwararar marasa lafiya.
Duk da yake ba a sa ran annobar za ta kai ƙololuwarta har zuwa watan gobe, hukumomin lafiya sun bayyana damuwa game da ƙaruwa cikin sauri na mutanen da ke kamuwa.
An sake ƙaƙaba dokokin kulle a watan jiya ciki har da haramta sayar da barasa.
Fiye da sulusi na dukkanin masu cutar an ba da rahoton samunsu ne a Gauteng - cibiyar hada-hadar kuɗi ta Afirka ta Kudu, kuma lardin da cikin hanzari ya zama matattarar wannan annoba a ƙasar.
Tsattsaurar dokar kullen Afirka ta Kudu ta sanya a watan Afrilu da na Mayu ta janyo lafawar bazuwar ƙwayar cutar.