#RevolutionNow: An 'kama' masu zanga-zanga a Abuja da Lagos

Lokacin karatu: Minti 1

Jami'an tsaron Najeriya sun tarwatsa masu zanga-zangar Revolution Now a Abuja, babban birnin ƙasar.

Wani jigo a zanga-zangar ya ce an kama mutum aƙalla 60.

An kama wasu daga cikin masu zanga-zangar ne da safiyar Laraba a Dandalin Unity Fountain kafin dagaa baya a sake kama wasu a Shataletalen Berger da ke Utako.

'Yan sanda ba su bayyana laifukansu ba zuwa yanzu.

Shugaba ko kuma wanda ya ƙaddamar da zanga-zangar, Omoyele Sowore ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa jami'an tsaro sun ci zarafin masu macin.

Har wa yau, hotuna da bidiyon da aka yaɗa sun nuna yadda 'yan sanda suka harba hayaƙi mai sa hawaye a jihohin Legas da Ogun.

Masu zanga-zangar #RevolutionNow na ƙarƙashin wani maci da Omoyele Sowore ya jagoranta, wani tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya a zaɓen 2019.

Ya ƙaddamar da zanga-zangar ne a 2019 yayin da ya yi zargin cin hanci da rashawa a kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.