'Yan gudun hijirar Burundi sun buƙaci a mayar da su gida

'Yan gudun hijirar Burundi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai 'yan guudn hijira 430,000 'yan Burundi da ke zaune a ƙasashe maƙwabta

Wasu 'yan Burundi mazauna sansanonin 'yan gudun hijira a Rwanda sun roƙi shugaban ƙasarsu da ya haɗa gwiwa da Rwanda da kuma hukumar kula da 'yan gudun hijira ta UNHCR domin mayar da su gida.

Sai dai har yanzu babu wata yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu da kuma Majalisar Ɗinkinn Duniya game da mayar da su gidajen nasu.

Fiye da 'yan gudun hijirar Burundi 60,000 ne ke zaune a sansanin Mahama da ke gabashin Rwanda tun bayan rikicin da ya biyo bayan zaɓen tsohon shugaba Pierre Nkurunziza a wa'adi na uku.

Sama da mutum 300 ne na 'yan gudun hijirar suka saka hannu kan wasiƙar zuwa ga shugaban nasu, inda suka ce "'yan siyasa ne ke son su ci gaba da zama a sansanin saboda buƙatar kansu".

Emmanuel Bizimana, ɗaya daga cikin waɗnda suka rubuta wasiƙar, ya shaida wa BBC cewa "yanzu lokaci ya yi da za su koma gida".

"Mun bincika kuma mun ji yadda yanayi yake, mun san cewa ƙasarmu lafiya lau take yanzu/ Abin da ya sa muka rubuta wasiƙar kenan domin su taimaka mana mu koma gida."

A jawabinsa na kama mulki, Shugaba Evariste Ndayishimiye ya roƙi 'yan gudun hijirar da su koma gida, tun daga wannan lokaci, 2,000 sun koma daga Tanzania, a cewar alƙluman Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ya zuwa ƙarshen watan Yuni, hukumar 'yan gudun hijira ta lissafa mutum 430,000 'yan Burundi da ke zaune a maƙwabtan ƙasashe, kusan 8,000 sun koma tun daga farkon shekarar nan kuma kusan dukkansu daga Tanzania.