Guguwar Hanna ta dira a kudancin Texas mai fama da annobar korona

Asalin hoton, Reuters
Gawurtacciyar guguwar Hanna ta sauka a kudancin jihar Texas, inda jami'an Amurka ke gargaɗi game da ƙaruwar baƙin hadari da iska mai ƙarfi gami da mamakon ruwan sama.
Gwamnan jihar Greg Abbott ya ayyana saukar iftila'i cikin yankunan Texas 32, yana cewa annobar korona za ta ta'azzara ayyukan kai aukin gaggawa.
Guguwar Hanna ta sauka ne a tsibirin Padre ranar Asabar kuma a yanzu tana barna a yankin da ke tsakanin birnin Corpus Christi da Brownsville.
Da iska mai gudun fiye da kilomita 145 cikin sa'a guda, guguwar na kwashe rufin gidaje tana awon gaba da su.
Hanna dai guguwa ce da ke kan matakin farko, matsayi na asa-asa a mizanin auna gawurtar guguwa na Saffir-Simpson mai mataki biyar.
Yankunan na Amurka dai, na cikin mafi fama da annobar korona, kuma a yanzu sai ga wata sabuwar matsala da ke buƙatar ɗaukin gaggawa.
Mazauna yankunan da ke gabar ruwa a Texas, waɗanda ke da yiwuwar ambaliya sun saba da jigilar kwashe su, don kauce wa ɓarnar gawurtacciyar guguwa kamar Hanna.
Sai dai a bana suna fama da cutar korona da kuma gagarumin ƙaruwar adadin masu fama da annobar a faɗin jihar.
A birnin Corpus Christi, inda cutar ta fi ƙamari, fiye da mutum 400 cikin al'umma da ta kai yawan dubu 325 ne aka kai su asibiti ranar Juma'a.
Yanzu kuma suna fuskantar gawurtacciyar guguwa mai barazana ga rayuka.
An faɗa wa mazaunan wasu yankuna su fice daga gidajensu, yayin da magajin birnin ke neman mutane su kwashi takunkumai tun da suna iya zama tsawon kwanaki a matsugunnan wucin gadi.
A wani wurin kuma, wata guguwar ce cikin gabashin Pacific ke dira kan tsaunukan Hawai.
Ƙaƙƙarfar guguwar Douglas wadda ta kai mataki na huɗu a baya, tuni dai ta ɗan lafa. Jami'ai sun ce tana iya wucewa ta kusa ko ta saman tsaunukan da iska mai ƙarfi da kuma manyan igiyoyin ruwa.
Shugaba ya ayyana dokar ta-ɓaci a Hawaii.











